Dambarwar Masarauta: Gwamnatin Abba Ta Aika Sako ga 'Makiya Kano'
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana rashin jin daɗi kan yadda wasu 'yan Kano ke amfani da batun masarauta wajen neman fitina
- Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya yi zargin cewa akwai wasu masu son tayar da fitina, waɗanda ya kira ‘makiya Kano’
- Sai dai kwamishinan ya nanata cewa sarki guda ɗaya ne a jihar, kuma shi ne wanda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta naɗa bisa dokar ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Kano ta bayyana rashin jin daɗin yadda wasu da ta kira ‘makiya' jihar ke dagula hankalin mazauna.
Kwamishinan yaɗa labaran Kano, Kwamred Ibrahim Abdullahi Wayya, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a jihar.

Kara karanta wannan
Sanatan Bauchi ya ba mutane kunya da azumi, bidiyosa yana rabon kuɗi ya shiga intanet

Asali: Facebook
A bidiyon da aka wallafa a shafin Facebook na NNPP Kwankwasiyya, Kwamred Ibrahim Wayya ya zargi wasu da ya ce suna karyar kishin Kano tare da kokarin tayar da tarzoma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Abba ta caccaki wasu ‘tsagera’
Kwamishinan yada labaran Kano, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya ce mutanen Kano sun riga sun gano wasu da ke kokarin cutar da al’ummar jihar.
Ya ce:
"Lokaci ya yi da ya kamata ku farka daga barcin da kuke yi. Al’ummar Kano sun riga sun gane ku, kuma babu abin da za ku yi da zai dagula jihar Kano."
"Sanusi II ne Sarkin Kano" — Gwamnatin Abba
Kwamred Wayya ya bayyana cewa sarki guda ɗaya ne a Kano, wanda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta amince da nadinsa.
Ya ce Muhammadu Sanusi II ne halastaccen sarki a jihar, saboda haka ba za su damu da yunkurin wasu na neman tayar da zaune tsaye kan batun masarauta ba.
Ya ce:
"Sarakuna ba su da bukata, musamman Sarkinmu, Limaminmu, Halifa Muhammadu Sanusi II—sarki kuma jika sarki, ɗan boko kuma malami. Shi ne sarki a Kano, ko ana so ko ba a so."
Ya ƙara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne zababben gwamnan Kano, saboda haka duk hukuncin da ya yanke kan batun masarauta ya zauna daram.
Jam'iyyar APC ta caccaki gwamnatin Kano
A tattaunawarsa da Legit Hausa, Sakataren Yaɗa Labaran APC na Kano, Ahmed S. Aruwa, ya zargi Gwamnatin Abba Kabir Yusuf da neman tayar da hankula.
Ya ce gwamnatin ta aikata abubuwa da dama a baya da suka tabbatar da cewa ba gwamnati ba ce mai neman zaman lafiya.
Ahmed S. Aruwa ya ce:
"Kotu ta ce kowa ya tsaya a inda yake, amma su suka ce karya ne. Gwamna ya zo da kansa ya na gaya wa mutane cewa 'dagatai da waye su sayi dawaki,' su fito su gaida sarkinsu. Me hakan ke nufi?"
"Yana so ya haifar da rashin zaman lafiya ne, domin wanda aka yi wa shari’a, wanda kotu ta ce shi ne halastacce, kai ka ce ba ka yarda da shi. Kai ka fito, wancan ya fito, to menene makomar Kano?"
Kwamishinan ya jaddada cewa dole ne ‘yan Kano su kauce wa yaɗa labaran ƙarya da ke iya jefa jihar cikin rudani.
Ya bayyana cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba za ta amince da duk wani yunkuri na raba kawunan jama’a ta amfani da masarauta ba.
A yayin da ake ci gaba da samun martani daga bangarori daban-daban, wasu dattawan Kano sun fara kira da a dakatar da kalaman da ke iya haddasa rikici.
Wasu na ganin cewa gwamnatin Kano da jam’iyyar adawa na bukatar su zauna a teburin sulhu domin warware matsalar ba tare da ta kara tsananta ba.
Har ila yau, masana harkokin siyasa sun bayyana cewa yadda ake amfani da masarauta wajen tayar da ƙura a Kano ba shi da amfani ga cigaban jihar. Sun bukaci kowa ya mutunta doka, tare da barin kotu ta yanke hukunci kan halaccin nadin sabon sarki.
Gwamnatin Abba ta zauna da marayu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ƙara zage damtse wajen samar da ababen more rayuwa da ayyukan jin ƙai ga marayu.
Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan tallafa wa marayu, inda ya ba da umarnin a karbi takardun wasu daga cikinsu don ba su aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng