Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Ta'addan Lakurawa cikin Azumi, an Samu Asarar Rayuka

Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Ta'addan Lakurawa cikin Azumi, an Samu Asarar Rayuka

  • Dakarun sojoji masu aikin samar da tsaro a jihar Kebbi sun yi artabu da ƴan ta'addan ƙungiyar ta'addanci ta Lakurawa
  • Jami'an tsaron sun yi nasarar hallaka wasu ƴan ta'addan bayan sun samu bayanan sirri kan ayyukansu
  • Sojojin sun kuma yi nasarar ƙwato makamai masu yawa tare da raunata wasu daga cikin ƴan ta'addan a artabun da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Dakarun sojoji sun samu nasarar kashe wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar ƴan ta’addan Lakurawa ne guda biyu a jihar Kebbi.

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan na Lakurawa ne a yankin Rubin Bisa da Fana, a cikin ƙaramar hukumar Dandi ta jihar Kebbi.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Lakurawa a Kebbi
Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Lakurawa a jihar Kebbi Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartaswa ta gwamnatin jihar Kebbi, AbdulRahman Zagga, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kaduna: Miyagu sun farmaki masallaci ana tsaka da Sallah, an samu asarar rai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji ƴan Lakurawa

AbdulRahman Zagga bayyana cewa wasu mambobin ƙungiyar sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da aka ƙwato makamai masu yawa daga hannunsu.

Ya bayyana cewa samamen wanda aka gudanar a ranar Laraba, an yi shi ne bayan samun bayanan sirri da kuma rahotannin leƙen asiri da aka tattara.

Sannan ya ke cewa farmakin da aka kai kan ƴan ta'addan, ya biyo bayan koken da shugaban ƙaramar hukumar Dandi, Dokta Mansur Kamba, ya shigar dangane da ayyukan ƴan ta'addan Lakurawa a ƙauyukan Fana da Rubin Bisa.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar Lakurawa ta dade tana addabar al’ummar yankin da hare-hare da kuma ayyukan ta’addanci.

Ƴan ta'addan suna satar mutane domin neman kuɗin fansa, sace dabbobi da kuma kai hare-hare a kan mazauna yankunan.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa an samu nasarar kama wasu makamai masu haɗari daga hannun ƴan ta’addan da aka kashe, ciki har da bindigogi na zamani da alburusai.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji na tsaka da farautar Bello Turji, an cafke hatsabiban yan bindiga 2

Jami’an tsaro na ci gaba da bin sawun waɗanda suka tsere domin tabbatar da cewa an kawar da barazanar da suke yi wa yankin gaba daya.

Jami'an tsaro sun ba jama'a shawara

A wani ɓangare na ƙoƙarin ganin an tabbatar da tsaro a yankin, an buƙaci mutane da su riƙa bayar da hadin kai ta hanyar samar da bayanai da za su taimaka wajen kamo sauran ƴan ta’addan da suka tsere.

Gwamnatin jihar Kebbi ta yabawa dakarun sojojin bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya, tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da kasancewa masu lura da duk wani motsi na bata-gari a yankunansu.

Wannan farmaki da aka kai a Dandi na ɗaya daga cikin yunkurin da gwamnati ke yi domin fatattakar ƴan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da suke fama da matsalar tsaro.

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasara kan ƴan ta'addan ISWAP bayan sun yi yunƙurin kai wani hari a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun daƙile harin da ƴan ta'addan da suka kai a wani sansaninsu, inda fatattake su zuwa cikin daji bayan an yi gumurzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng