Kungiyar ’Yan Ta’addan ISWAP Ta Kai Hari Jami’ar Maiduguri da Ke Borno?

Kungiyar ’Yan Ta’addan ISWAP Ta Kai Hari Jami’ar Maiduguri da Ke Borno?

  • Rundunar tsaro a Maiduguri ta karyata jita-jitar harin ISWAP a Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) da ke jihar Borno
  • Jami'an sun bayyana cewa harbe-harben da aka ji sun faru ne a Ajilari, ba a harabar jami’a ba da ke Maiduguri
  • An samu wasu sojoji sun dakile harin 'yan kungiyar ISWAP, sun kashe 'yan ta'adda tare da kwato bindigogi biyu
  • Hukumomi sun bukaci jama’a su daina yada ƙarya kuma su nemi bayanai daga sahihan majiyoyi masu tushe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Hukumar tsaro da ke Maiduguri ta yi martani kan jita-jitar kai hari jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno.

Hukumomin tsaro sun karyata rahoton cewa 'yan ta'addan ISWAP sun kai wani hari a harabar Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) da ke jihar.

Jami'an tsaro sun yi martani kan hari a jami'ar Maiduguri
Hukumomin tsaro a Maiduguri sun karyata rahoton kai hari jami'ar Maiduguri. Hoto: Legit.
Asali: Original

Martanin jami'an tsaro kan hari a jami'ar Maiduguri

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Bayan fama da jinya, shugabar karamar hukuma ta rasu a Ramadan

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa babu labarin kai harin da ake ta yadawa inda ya ce rahoton karya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu rahotanni da suka karade kafafen sada zumunta sun yi zargin cewa an kai hari jami’ar, amma jami’an tsaro sun ce wannan batu ba gaskiya ba ne.

Sun tabbatar da cewa:

"Duk bangarorin jami'ar lafiya suke, kuma dalibai na ci gaba da harkokinsu ba tare da tsoro ba.”
An karyata kai hari jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno
Jami'an tsaro sun fadi abin da ya faru kan jita-jitar kai hari jami'ar Maiduguri. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Abin da ya faru kan jita-jitar da ake yadawa

Hukumar tsaro ta bayyana cewa harbe-harben da aka ji kwana huɗu da suka wuce ba a cikin jami’a suka faru ba.

An ce 'yan ta'addan ISWAP sun yi yunkurin kutsawa unguwar Ajilari, wacce ke nesa da jami’ar a cikin karamar hukumar Jere.

Sojoji sun ce sun gaggauta mayar da martani, suka tarwatsa 'yan ta’addan, suka kashe da dama, sannan suka kwato bindigu biyu.

Kara karanta wannan

Bayan raddin Fubara ga Tinubu, 'yan sanda sun yi gargadi mai zafi a Rivers

Sun ce an yi nasarar kwato makamai daga hannunsu, an kuma dawo da zaman lafiya cikin yankin.

Jami’an tsaron sun ce ba a kai hari jami’a ba, don haka jama’a su daina yada jita-jita da ke haddasa fargaba.

Jami'an tsaro sun ce:

“Dukan yankunan na cikin natsuwa, dalibai da mazauna wurin su kwantar da hankalinsu, rundunar tsaro na nan a shirye.”
“Kar ku yada jita-jita da ba a tabbatar da ita ba domin hakan na haddasa firgici.”

Sun kuma bukaci jama’a su dogara da sahihan hanyoyi wajen samun bayanai domin samun kwanciyar hankali kan lamuran tsaro.

Sun ce za su ci gaba da kawo karin bayani idan an samu sababbin abubuwa dangane da abin da ke faruwa.

An daka wawa kan motar abinci a Borno

Kun ji cewa wasu matasa da ba a san ko su wanene ba sun kwace wata motar tallafin kayan abinci ta hukumar WFP a jihar Borno.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya dauko ruwan dafa kansa bayan kiran 'yan majalisar Kaduna 'jalilai'

An ce motar na kan hanyar zuwa Damasak lokacin da direbanta ya tsaya a gefen hanya, babu kowa a ciki yayin da aka yi aika-aikan.

Rahotanni sun ce an sace buhunan shinkafa, gishiri, sukari, wake da kuma man gyada wanda ba a san yawan asarar da aka yi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng