Kaduna: Miyagu Sun Farmaki Masallaci ana tsaka da Sallah, an Samu Asarar Rai
- An shiga jimami bayan wasu ƴan daba sun kai farmaki a masallaci ana tsaka da gudanar da Sallah a jihar Kaduna
- Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna tabbata da aukuwar lamarin wanda ya auku a ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu
- Kakakin ƴan sandan jihar ya bayyana cewa an cafke mutum 12 da ake zargin suna da hannu a kai harin da aka yi
- ASP Mansir Hassan ya ƙara da cewa ƴan daban sun hallaka mutum ɗaya bayan sun yi amfani da wuƙa wajen farmakarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta kama mutum 12 da ake zargi da kai hari a wani masallaci.
Ƴan daban ana kuma zarginsu da kashe wani mutum ɗaya a yankin Tudun Wada, ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.

Asali: Original
Kakakin rundunar jan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Sojoji na tsaka da farautar Bello Turji, an cafke hatsabiban yan bindiga 2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan daba suka kai farmaki a masallaci
Ya ce ƴan daba daga Malalin Gabas, Tudun Wada, Rafin Guza da Unguwar Baduko ne suka kai hari kan wasu musulmai da ke gudanar da sallar Tahajjud.
Lamarin ya faru ne a Layin Bliya, Hanyar Makwa Road, Rigasa, da misalin karfe 2:00 na dare a ranar Juma’a.
A cewarsa, kafin isowar jami’an tsaro da dakarun CJTF, ƴan daban sun kashe wani matashi mai shekara 28, mai suna Usman Mohammed, ta hanyar daɓa masa wuƙa, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Bayan faruwar lamarin, jami’an ƴan sanda sun yi gaggawar damke mutum 12 waɗanda suka amsa laifinsu, sannan kuma an kwace makamai da dama daga hannunsu.
Rundunar ƴan sandan ta ce an ƙaddamar da cikakken bincike domin gano hakikanin yadda lamarin ya faru, tare da tabbatar da cewa an yi adalci.
Ƴan sanda sun ƙara tsaurara tsaro
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa an ƙara yawan jami’an tsaro a wuraren da ake gudanar da sallah, musamman masallatai domin kare lafiyar jama’a.
Rundunar ta kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu kula da tsaro, tare da gaggauta sanar da ƴan sanda idan suka ga wani abu na zargi domin hana aikata laifuffuka.
Daga ƙarshe, ƴan sandan sun gargaɗi dukkan ƴan daba da su daina aikata miyagun laifuffuka, ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani idan aka kama su.
Ƴan bindiga sun kai farmaki a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki a a wasu ƙauyukan jihar Kaduna.
Ƴan bindigan sun kai farmakin ne a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar a cikin tsakar dare yayin da mutane suke barci a gidajensu.
Tsagerun ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutum 10 a hare-haren da suka kai cikin ƙauyukan guda uku na ƙaramar hukumar.
A yayin farmakin da ƴan bindigan suka kai, sun kuma jikkata wasu mutane da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng