Kotu Ta Raba Gardama kan Karar Neman Tsige Mai Martaba Sarkin Zazzau
- Kotun daukaka kara da ke Kaduna ta yi watsi da karar da ke neman tsige Sarkin Zazzau na 19, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli
- Tubabben Wazirin Zazzau, Ibrahim Mohammed Aminu, ya kai karar bisa zargin rashin bin doka wajen nadin sarkin da aka yi
- Kotun ta bayyana cewa karar ba ta da inganci don haka ba za a ci gaba da sauraren ta ba, kuma ta ce babu uzuri
- Wakilin Sarki ya ce hukuncin ya tabbatar da gaskiya, yayin da lauyan mai kara ya ce za su duba hukuncin kafin daukar mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zaria, Kaduna - Kotun daukaka kara da ke zaune a Kaduna ta yi hukunci kan neman tsige Mai martaba Sarkin Zazzau.
Kotun ta yi watsi da karar da ke neman a tsige Sarkin Zazzau na 19, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a ranar Alhamis 20 ga watan Maris, 2025.

Asali: Facebook
Masarautar Zazzau: Wane hukunci kotun ta yanke?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin masarautar Zazzau ya wallafa a manhajar X a jiya Alhamis 20 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mai zaben sarki a masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Mohammed Aminu, ne ya shigar da karar, yana kalubalantar nadin da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi a 2020.
Aminu wanda shi ne tubabben Wazirin Zazzau, ya ce ba a bi ka’ida wajen nadin sarkin ba, ya kuma bukaci kotu ta soke nadin a kotun jiha, wadda ta yi watsi da karar.
Kotun daukaka karar ta yanke hukunci cewa karar ba ta da inganci, ma’ana an shigar da ita bayan lokacin da doka ta amince ya wuce.
Kotun ta kuma yi watsi da rokon da ke neman a yi amfani da uzuri na musamman, tana mai cewa ba ta shige cikin dokokin da za su ba da rangwame ba.

Asali: Facebook
Martanin Wazirin Zazzau kan hukuncin kotu
Yayin martaninsa, Wazirin Zazzau, Khadi Muhammad Inuwa, ya ce masarautar ta gamsu da hukuncin, wanda ya kira nasara ce ga adalci da tsarin shari’a.
Lauyan wanda ya shigar da kara, Muhammed Tajudeen Muhammed, ya ce zai duba hukuncin sosai domin sanin matakin da ya kamata su dauka.
Tajudeen ya ce abokin aikinsa na kokarin tabbatar da cewa an karya doka da al’ada wajen nadin sarkin, amma kotu ba ta amince da hakan ba.
Shi kuwa lauyan Sarkin Zazzau, Abdul Ibrahim (SAN), ya ce sun karɓi hukuncin da farin ciki, ya ce kotun daukaka kara ta yi watsi da karar gaba ɗaya.
Ya bayyana hukuncin a matsayin tabbaci mai karfi cewa nadin Sarkin Bamalli ya cika ka'ida, kuma hakan hujja ce ga bin tsarin mulki da shari’a.
Sarkin Zazzau ya nada Magajin Rafi
Kun ji cewa Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya nada sabon Magajin Rafin Zazzau bayan rahotanni sun ce mai rike da sarautar ya yi murabus.
An ce basaraken ya nada Alhaji Shehu Abdullahi mai shekaru 61 a matsayin wanda zai rike sarautar, ya gaji Farfesa Ango Abdullahi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng