Rikicin Rivers: Sabuwar Matsala Ta Kunno kai Tsakanin Majalisar Wakilai da Tinubu

Rikicin Rivers: Sabuwar Matsala Ta Kunno kai Tsakanin Majalisar Wakilai da Tinubu

  • Majalisar Wakilai ta amince da dokar ta-baci a Rivers, amma ta yi gyare-gyare, ta umarci shugaban riko ya rika kai rahoto gare su kai tsaye.
  • 'Yan majalisar sun dage cewa kundin tsarin mulki bai bai wa Majalisar Zartarwa iko ba, don haka gare su shugaban riko ya dace ya rika biyayya
  • Majalisar ta bukaci a samu sassaucin wa’adin dokar ta-baci, tare da kafa kwamitin sulhu da zai kunshi irinsu Janar Abdulsalami Abubakar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-baci a jihar Rivers, amma ta yi wasu gyare-gyare a matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka.

'Yan majalisar sun dage kan cewa shugaban riko da aka nadawa Rivers zai rika kai rahoto kai tsaye ga majalisar tarayya, ba ga majalisar zartarwa ta tarayya ba.

Kara karanta wannan

"Ka da a ɗora mun laifi": Gwamna Fubara ya cire tsoro, ya ƙaryata kalaman Tinubu

Majalisa ta gyara bukatar Tinubu da ke cikin dokar ta baci da ayyana a Rivers
Majalisar wailai ta ce shugaban riko Rivers zai kai rahoto gare ta ba ga majalisar zartarwa ba. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisa ta ki amincewa da bukatar Tinubu

Majalisar ta yi amfani da sashe na 11(4) na kundin tsarin mulki, wanda ke bai wa majalisar tarayya ikon karɓar aikin majalisar jiha idan ta kasa aikinta, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Etanabene Benedict, ɗan majalisa daga Delta, kundin tsarin mulki ya tanadi cewa majalisar tarayya ce ke da hakkin jagorancin majalisar jiha, ba FEC ba.

Bayan jin bahasi, majalisar ta amince da wannan gyara, inda ta umarci Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas ya rika kai rahoto kai tsaye ga majalisar ba ga Shugaba Bola Tinubu ba.

Majalisar ta bukaci duba wa'adin dokar ta-baci

Majalisar wakilan ta bukaci a samu sassaucin duba wa'adin dokar ta-bacin, maimakon barin ta na tsawon watanni shida kamar yadda shugaban ƙasa ya ayyana.

Ali Isah, mataimakin bulalar marasa rinjaye, ya ce akwai bukatar a bude kofar janye dokar idan an cimma zaman lafiya kafin wa’adin ya cika.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, majalisa ta ɗauki matsaya kan dokar ta ɓaci da Tinubu ya ayyana a Rivers

Ya bayyana cewa idan bangarorin da ke rikicin suka taru cire duk wani bambanci tsakaninsu, za a iya cimma sulhu cikin kankanin lokaci.

Mataimakin bulalar majalisar ya ce:

“Idan shugabanni sun nuna jajircewa, ba sai mun jira tsawon watanni shida ba, ana iya kawo ƙarshen matsalar cikin mako ɗaya ko biyu.”

Shawarar samar da kwamitin sulhu

Majalisar wakilai ta magantu kan kafa kwamitin sulhu don magance rikicin Rivers
Majalisar wakilai ta amince da kafa kwamitin sulhu domin magance rikicin Rivers. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisar wakilai ta kuma bukaci kafa kwamitin sasanci da zai kunshi 'yan majalisar tarayya da manyan mutanen Najeriya.

Daga cikin waɗanda aka bukaci su shiga kwamitin akwai tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar da Bishof Hassan Kukah.

A cewar majalisar, kwamitin zai shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin cikin zaman lafiya yayin da ake karkashin dokar ta-baci.

Majalisar ta amince cewa matakin zai taimaka wajen cimma daidaito tsakanin bangarorin da ke rikici a jihar Rivers.

Da wannan mataki, ana fatan dokar ta-baci ba za ta dauki dogon lokaci ba, idan aka cimma zaman lafiya cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Fubara ya karyata zarge-zargen Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Siminalayi Fubara ya musanta zargin shugaba Bola Tinubu cewa ya rusa majalisar dokokin Rivers ba tare da sake gina ta ba.

Ya bayyana cewa yana daukar matakan kare albarkatun mai na jihar, kuma sabuwar majalisar dokoki ta kusa kammala gini da kashi 80%.

Fubara ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da tayar da rikici a Rivers ta hanyar yin kalaman da suka fusata ‘yan kabilar Ijaw.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel