Bayan Raddin Fubara ga Tinubu, 'Yan Sanda Sun Yi Gargadi Mai Zafi a Rivers
- Rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun dauki matakan gaggawa don tabbatar da tsaro a Jihar Rivers
- Rahotanni sun nuna cewa an tura karin jami’an tsaro da kayan aiki don dakile duk wata barazana ga zaman lafiya
- ‘Yan sanda sun gargadi duk masu yunkurin tayar da tarzoma a jihar da cewa za su fuskanci hukunci mai tsauri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, jami’an tsaro sun dauki matakan hada kai domin kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.
A cewar rundunar ‘yan sanda, tun kafin ayyana dokar ta-baci, sun riga sun lura da matsalolin tsaro da barazanar da ke kara kamari a jihar.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da rundunar 'yan sanda ta yi ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tura karin jami’an tsaro zuwa jihar Rivers
Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, ya ba da umarnin tura karin jami’an tsaro da kayan aiki domin tabbatar da tsaro a Jihar Rivers.
Rundunar ta ce wannan yunkuri an yi shi ne tare da hadin gwiwar dakarun soji da sauran hukumomin tsaro domin hana barkewar tashin hankali.
‘Yan sanda sun tabbatar da cewa za su tabbatar da kare rayukan jama’a da kadarorin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu a jihar.
Rundunar ta bukaci ‘yan kasa da su ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali tare da kiyaye doka da oda.
Rivers: An gargadi masu tayar da tarzoma
A cikin sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, an gargadi duk masu yunkurin haddasa tarzoma da cewa za su fuskanci hukunci mai tsauri.
Hukumar ta ce duk wanda ke da korafi kan matakin da aka dauka, ya na da damar bin hanyoyin da doka ta tanada don neman hakkinsa.
Haka zalika, ‘yan sanda sun bayyana cewa duk wani yunkuri na tayar da bore ko gangami na hana zaman lafiya za a dakile shi tare da hukunta masu hannu a ciki.

Asali: Facebook
Rundunar ta bukaci jama’a da su ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali tare da gujewa duk wata fitina da ka iya haddasa rashin tsaro.
Bukatar fadakar da jami’an tsaro
Rundunar ‘yan sanda ta bukaci ‘yan Najeriya, musamman mazauna Jihar Rivers, da su kasance masu lura da duk wani abu da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya.
Jami’an tsaro sun nemi al’umma da su rika kai rahoton duk wani motsi na bata-gari domin a dauki matakin gaggawa.
A cewar ‘yan sanda, duk wani mutum ko kungiya da ke shirin haddasa hargitsi a Jihar Rivers ya janye daga shirinsa ko kuma ya fuskanci hukunci.
Rundunar ta ce jami’an tsaro sun shirya tsaf domin tunkarar duk wani kalubale da ka iya tasowa, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Kwankwaso ya yi magana kan rikicin Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da matakin dakatar da zababbun shugabanni a Rivers.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce matakin ya saba dokar kasa kuma zai iya zama barazana ga tsarin mulkin dimokuradiyya a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng