'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Sojoji a Wani Kazamin Farmaki da Suka Kai Benuwai

'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Sojoji a Wani Kazamin Farmaki da Suka Kai Benuwai

  • ‘Yan bindiga sun kai hari a garuruwan Benuwai, inda suka kashe mutum biyar, ciki har da sojoji biyu, lamarin da ya jefa yankin cikin fargaba
  • An kai harin ne a ƙauyukan Mgbaigbe da Mbaitye, inda ‘yan bindiga suka yi wa sojojin sintiri kwanton ɓauna, sannan suka farmaki fararen hula
  • Shugaban ƙungiyar Mdzou U Tiv, Iorbee Ihagh, ya bukaci al’ummar yankin da su kare kansu, ya na zargin Fulani da ƙoƙarin mamaye Tibi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benuwai - ‘Yan bindiga sun sake kai hari garuruwa biyu a ƙaramar hukumar Kwande ta jihar Benue, sun kashe mutum biyar ciki har da sojoji biyu.

Gwamnatin jihar ta yi Allah-wadai da harin, tare da jimamin mutuwar waɗanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan farmaki.

Gwamnatin Benuwai ta tabbatar da kisan sojoji 2 da farar hula a wani harin 'yan bindiga
'Yan bindiga sun kashe sojoji da farar hula a sabon farmakin da suka kai Benuwai. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun kashe sojoji a Benuwai

Kara karanta wannan

Mashahurin ɗan kasuwa kuma malami a Kano, Nasiru Ahali ya rasu a shekara 108

A cewar mazauna yankin, hare-haren sun shafi ƙauyukan Mgbaigbe da Mbaitye, waɗanda ke kusa da hedikwatar Turan a Jato Acka, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi wa sojojin sintiri kwanton ɓauna, inda suka kashe su tare da far wa al’umma.

Yankunan Moon, Mbaikyor, Mbadura, Kumakwagh, da Yaav na ƙasar Turan sun sha fuskantar irin wannan hari, wanda ya tilasta wa mazauna tserewa zuwa Jato Acka.

Shugaban ƙungiyar 'yan asalin kabilar Tiv ta duniya, watau Mdzou U Tiv, Iorbee Ihagh, ya tabbatar da harin ga jaridar Punch.

An nemi mutane su kare kansu daga 'yan bindiga

Iorbee Ihagh, wanda tsohon kwanturola ne a gidan gyaran hali, ya bukaci al’ummar Benue da su shirya domin kare kansu daga irin waɗannan hare-hare.

Ya nuna damuwa kan yadda makiyaya ke ƙara karfi a yankin, yana mai cewa suna ƙoƙarin mamaye ƙasar Tiv gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mahaddacin Kur'anin da suka sace a Katsina? An gano gaskiya

Iorbee Ihagh ya bayyana cewa Jato Acka na da muhimmanci ga al’ummar Tiv, kamar yadda Ile-Ife ke da muhimmanci ga kabilar Yarbawa.

Haka nan, Ihagh ya jinjinawa Gwamna Hyacinth Alia kan ƙoƙarinsa na ci gaban jihar, amma ya bukaci ƙarin matakai don kare rayuka da dukiyoyi.

Ya kuma bukaci a farfaɗo da hanyoyin tsaron gargajiya, yana mai cewa:

“A ƙarni na 19, al’ummar Tiv sun yi galaba kan Fulani a yaƙin Jihadi ta amfani da kibau masu guba."

Gwamnatin Benuwai ta yi jimamin kisan sojojin

Gwamnatin Hyacinth Alia ta tabbatar da kisan sojoji a harin da 'yan bindiga suka kai Benuwai
Gwamnatin Benuwai ta yi jimamin kisan sojoji a harin 'yan bindiga. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Facebook

Mai ba gwamna shawara kan tsaro da harkokin cikin gida, Joe Har, ya tabbatar da harin amma ya ce bai samu cikakken bayani daga sojojin yankin ba.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Benue, Catherine Anene, ta ce su na bibiyar rikicin, amma ba ta tabbatar da yawan waɗanda suka mutu ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza fada da 'yan bindiga, sun hallaka miyagu a Zamfara

Gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar sojojin biyu, inda mataimakin gwamna, Sam Ode, ya bayyana hakan yayin taron majalisar zartarwa.

Ode ya nuna jimami kan mutuwar sojojin, ya na mai cewa sun rasa rayukansu ne yayin da suke kare fararen hula a ƙaramar hukumar Kwande.

'Yan bindiga sun hallaka sojoji 22 a Delta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, aƙalla sojoji 22 ne ‘yan bindiga suka kashe a ƙauyen Okuoma da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu, jihar Delta.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa sojojin Bataliya ta 181, Bomadi, sun je aikin ceto ne lokacin da ‘yan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna suka hallaka su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng