'Ayi Hankali': Abin da Shugaban Rikon Kwarya Ya Fada bayan Shiga Ofis a Rivers
- Sabon shugaban rikon kwarya a Rivers, Ibok-Ete Ibas, ya bayyana kansa a matsayin dan yankin, yana mai sha'awar dawo da zaman lafiya
- Ibas ya gargadi mazauna jihar da su guji ta da fitina da lalata man fetur, inda ya jaddada illar hakan ga tattalin arziki da muhalli
- Ya yaba da matakin shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-baci da cewa hakan zai dawo da doka da ci gaban tattalin arziki
- Ibas ya ce zai yi aiki da dukkanin bangarori don tabbatar da zaman lafiya da dorewar dimokuradiyya a jihar Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Shugaban rikon kwarya a Jihar Rivers, Ibok-Ete Ibas, ya tabbatar da cewa shi ba dan siyasa ba ne amma zai tabbatar da zaman lafiya.
A jawabin da ya gabatar a gidan gwamnati a Port Harcourt, Ibas ya ce yana da niyyar kare ‘yancin jama’a da tsaron lafiyarsu.

Asali: Twitter
Ibok-Ete Ibas ya gargadi al'ummar jihar Rivers
Sai dai ya yi gargaɗi mai tsanani kan lalata albarkatun mai da tashin hankali, yana rokon jama’a su guji komawa ga rikice-rikicen da suka gabata, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban rikon kwaryar ya ce ya sadaukar da rayuwarsa wurin yi wa kasa hidima lokacin da yake hafsan sojojin ruwa.
Ya ce:
“Na sadaukar da rayuwata don hidimar kasa, tun daga matsayin Hafsan Sojojin Ruwa har zuwa Jakadan Najeriya a Ghana.
“Ni ɗa ne na yankin Neja Delta, ina jin radadin wannan rikici kan iyalai, kasuwanci da makomar mutanenmu."
Ibok-Ete Ibas ya ce rikicin siyasa da ke ci gaba da faruwa a jihar babban cikas ne ga shugabanci da dimokuradiyya da kuma cigaban al’umma.
Ya kara da cewa:
“Abin da aka dora min shi ne dawo da doka da oda, da zaman lafiya da kuma samar da yanayi mai kyau ga tattalin arziki.
“Yankin Neja Delta ya wuce zamanin lalata kayan man fetur, ya kamata mu guji komawa irin ta da hankali a wadannan lokutan."

Asali: Twitter
Wace shawara Ibok-Ete Ibas ya ba 'yan Rivers?
Ibok-Ete Ibas bukaci jama’a su guji kai hari kan kayan mai, ya na tunatar da illar da hakan ke yi ga muhalli da cigaban tattalin arziki.
Ya ce za a mutunta ‘yancin jama’a da bin doka, amma za a hukunta duk wanda ya saba doka ko ya tayar da hankali.
Ya yi godiya ga shugaba Tinubu saboda amincewa da shi, sannan ya yaba wa Majalisar Tarayya kan amincewa da dokar ta-baci.
“Ba za mu yi amfani da iko ba tare da dalili ba, amma za mu hukunta duk wanda ya kawo barazana ga zaman lafiya.
Ibok-Ete Ibas: Abubuwan sani kan shugaban rikon kwarya
Kun ji cewa bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) a matsayin shugaba na rikon kwarya a jihar Rivers.
Legit Hausa ta yi bincike kan muhimman abubuwa game da sabon shugaban kama daga haihuwa, karatu zuwa shugabancin sojojin ruwa da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng