Yadda Sheikh Pantami Ya Kubuta daga Sharrin 'Yan Fashi bayan Harbi 3 a Titi
- Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana yadda ya fuskanci ‘yan fashi a kan hanya daga Gombe zuwa Borno
- Malamin ya ce ‘yan fashin sun tare su a kusa da Damboa, inda ya yi arangama da su yayin da daya daga cikinsu ya sa masa bindiga
- Sheikh Pantami ya ce addu’ar HasbunAllahu wa ni’imal wakil ce ta kubutar da shi daga hannun ‘yan fashin yayin da suka yi arangama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami ya bada labarin yadda ya tsallake hatsarin ‘yan fashi a wata tafiya da ya yi daga Gombe zuwa Borno.
Malamin ya bayyana haka ne yayin tafsirin Ramadan na bana, a rana ta 19, inda ya ce lamarin ya faru ne a yankin Damboa.

Asali: Facebook
A bidiyon tafsirin da aka wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Pantami ya ce addu’ar HasbunAllahu wa ni’imal wakil ce ta taimaka masa wajen kubuta daga hannun ‘yan fashin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Arangamar Sheikh Pantami da ‘yan fashi
Sheikh Pantami ya bayyana cewa ya tafi daga Gombe zuwa Borno domin kai wani yaro asibiti sakamakon ciwon ido da yake fama da shi.
A yayin tafiyarsu, sun isa wani wuri da hanyar ba ta da kyau a Damboa, inda ‘yan fashi suka tare motarsu suka hana su wucewa.
Malamin ya ce a lokacin da aka tare su ya na barci a cikin mota, sai kawai ya farka ya na ganin bindiga a kusa da kansa.
Ya na firgita sai ya buge bindigar dan fashin, wanda ya fusata ya ce:
"Za ka kwace min bindiga ne?"
Addu’a ta yi sanadiyyar kubutar Pantami
A cikin dambarwar da ta kaure tsakaninsa da dan fashin, Sheikh Pantami ya rike bindigar ba tare da ya sake ta ba, har aka yi harbi sau uku.
Bayan haka, ‘yan fashin suka bukaci kowa ya fito daga mota, yayin da daya daga cikinsu ke cewa:
"Kai ne ko? Na gane kalar rigarka."
Sai dai a lokacin da aka fito daga motar, ‘yan fashin sun kasa gane Sheikh Pantami, duk da cewa sun ce sun san irin rigar da yake sanye da ita.
Sheikh Isa Ali Panatami ya ce ba abin da yake fada a lokacin sai kawai HasbunAllahu wa ni’imal wakil.
Pantami ya samu matsala a jirgin sama
Sheikh Pantami ya kuma bada wani labari na yadda jirgin sama da yake ciki daga Abuja zuwa Maiduguri ya shiga cikin matsala a sararin samaniya.
Ya ce sun taso daga Abuja amma jirgin bai iya sauka ba, yana ta yawo a sama har jama’a suka firgita.

Asali: UGC
Malamin ya ce a lokacin ya bukaci kowa ya rika fadin HasbunAllahu wa ni’imal wakil domin rokon Allah ya kubutar da su.
Bayan sun yi haka, cikin ikon Allah, an shawo kan matsalar, jirgin kuma ya sauka lafiya a Maiduguri.
Sakon Sheikh Pantami ga al’umma
Daga karshe, Sheikh Pantami ya bukaci Musulmai da su saba da fadin HasbunAllahu wa ni’imal wakil a duk lokacin da suka shiga cikin wata matsala.
Ya ce wannan addu’a tana da matukar tasiri wajen tsira daga hadura da kuma neman kariyar Allah a kowane lokaci.
Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci a duniya kuma masanin hadisi, Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini ya rasu a Masar.
Legit ta rahoto cewa Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini ya rasu ne bayan shafe shekaru 69 a duniya, kuma ya kasance cikin yi wa addini hidima tsawon rayuwarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng