'Ba Mu Yarda Ka Ƙara Wa'adin Dokar Ta Ɓaci ba': Amsar Majalisa ga Jonathan a 2014

'Ba Mu Yarda Ka Ƙara Wa'adin Dokar Ta Ɓaci ba': Amsar Majalisa ga Jonathan a 2014

  • A 2014, majalisar wakilai ta ƙi amincewa da buƙatar Shugaban kasa Goodluck Jonathan na tsawaita dokar ta-ɓaci a jihohin Arewa maso Gabas
  • A 2013, Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a Borno, Yobe da Adamawa domin dakile hare-haren Boko Haram da kuma maido da doka da oda
  • Majalisar ta hana tsawaita dokar a karo na uku, inda Jonathan ya gaza samun rinjayen ƙuri’un da ake buƙata a ranar 20 ga Nuwamban 2014

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A shekarar 2014, majalisar wakilai ta ƙi amincewa da buƙatar Shugaba Goodluck Jonathan na ƙara wa’adin dokar ta-ɓaci a jihohin Arewa maso Gabas.

A ranar 14 ga Mayu, 2013, Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a Borno, Yobe da Adamawa domin dakile hare-haren Boko Haram da ke ƙara ta’azzara.

Kara karanta wannan

Majalisa dattawa ta dauki mataki kan dokar ta bacin da Tinubu ya sa a Rivers

Yadda majalisa ta ki amince da bukatar Jonathan na tsawaita wa'adin dokar ta baci a jihohin Arewa 3
Tuna baya: Yadda Jonathan ya gaza samun rinjayen majalisa wajen tsawaita wa'adin dokar ta baci a 2014. Hoto: @GEJonathan, @HouseNGR
Asali: Twitter

2014: Majalisa ta ki yarda da bukatar Jonathan

Ya dauki matakin ne da nufin maido da doka da oda, tare da hana ‘yan ta’adda mamaye yankunan da suke mayarwa karkashin ikon su, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan wa’adin watanni shida na farko ya cika a Nuwamban 2013, majalisa ta amince da ƙarin wa’adi sau biyu, a Nuwa/mba 2013 da Mayun 2014.

Sai dai, a Nuwamban 2014, majalisar wakilai ta ƙi amincewa da ƙarin wa’adi na uku, ta hana Jonathan samun rinjayen ƙuri’un da ake buƙata.

A ranar 20 ga Nuwamba, 2014, Jonathan ya gaza samun kaso biyu bisa uku na goyon bayan ‘yan majalisa, wanda ya kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a jihohin bayan watanni 18.

'Yan majalisa sun yi turmutsun tsallake katanga

Lokacin da majalisa ta taru don tattaunawa kan buƙatar Jonathan, jami’an tsaro sun yi shinge a harabar majalisar, suka hana wasu ‘yan majalisa shiga.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai ta ɗauki zafi kan buƙatar Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

Sakamakon haka, wasu ‘yan majalisa ciki har da shugaban majalisar na lokacin, Aminu Waziri Tambuwal, suka haura katanga don shiga cikin zaure taron.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, ‘yan majalisar Arewa maso Gabas suka nuna adawarsu, suna masu cewa dokar ta-ɓaci ta jawo ƙara tabarbarewar tsaro ne a yankin.

Wannan lamari, ya sa ‘yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye a dakin taron bayan samun rikici da magoya bayan Tambuwal sama da 200 da aka hana shiga.

Kalubalen da ake tunanin Tinubu zai fuskanta

Majalisar tarayya na duba yiwuwar amincewa da bukatar Tinubu na ayyana dokar ta baci a Rivers
Majalisar tarayya ta shirya duba bukatar Tinubu kan ayyana dokar ta baci a Rivers: @HouseNGR, @officialABAT
Asali: Twitter

A ranar 18 ga Maris, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers sakamakon rikicin siyasa da ya ki ci ya ki cinyewa.

Bayan haka, Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Dokar kasa ta tanadi cewa, kafin dokar ta-ɓaci ta fara aiki, dole ne shugaban ƙasa ya aikawa da shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Fubara na iya dawowa: Tinubu na fusƙantar barazana kan dokar ta baci a majalisa

Ana ta ce-ce-ku-ce kan tushen ikon shugaba Tinubu na dakatar da gwamna da ‘yan majalisa, kasancewar kundin tsarin mulki bai fayyace hakan ba.

Domin amincewa da dokar, Tinubu na buƙatar kuri’u 240 daga cikin ‘yan majalisar wakilai 360 da kuma 73 daga cikin sanatoci 109.

A gefe guda, akalla sanatoci 36 ne ake buƙata domin hana amincewa da dokar, yayin da ‘yan majalisa 121 za su iya kawar da ita.

Majalisar wakilai ta amince da bukatar Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar wakilai ta kawo karshen ce-ce-ku-ce, bayan da ta amince da dokar ta bacin da shugaba Bola Tinubu ya ayyana a Rivers.

‘Yan majalisa 243 ne suka halarci zaman da ya amince da bukatar shugaba Tinubu, bayan sun kada ƙuri’ar baki kamar yadda shugabansu, Tajudeen Abbas ya bayyana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng