Rigima Ta Ɓarke a Jihar Kano da FAAN Ta Fara Rusa Gidajen Mutane a Watan Azumi
- Hukumar FAAN ta fara rusa gine-gine a rukunin gidajen 'Aviation Quaters' da ke jihar Kano, lamarin da ya haifar da hayaniya
- Mazauna unguwar sun ce tun 2021 gwamnatin tarayya ta sayar masu da gidajen amma kwatsam FAAN ta fara ƙoƙarin ƙwace masu
- A nata ɓangaren, FAAN ta jaddada cewa an gina gidajen ne domin ma'aikatan filayen jirgin sama, ba don wasu daban ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta fara rushe gine-gine da gidajen mutane a rukunin gidajen Aviation Quaters da ke a Kano.
Wannan lamarin da ya faru a watan azumi ya jawo ce-ce-ku-ce da rigima tsakanin mazauna yankin da hukumar kan haƙƙin mallaka.

Asali: Facebook
Daily Trust ta ce mazauna wurin sun nuna damuwa kan matakin da FAAN ta ɗauka saboda a cewarsu ya saɓawa yarjejeniyar da suka yi da gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna sun yi fatali da matakin FAAN
Da yake magana a madadin mazauna da lamarin ya shafa, Obadaki Muhammad Mustapha, ya ce rushen-rushen da hukumar ke yi ya saɓawa umarnin gwamnati domin ta amince su sayi gidajen.
Obadaki Muhammad, ma'aikacin Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) kuma sakataren kwamitin unguwar ya ce tun 2011 suka fara tattaunawa kan mallakar wurin.
A cewarsa, tun daga 2011 ne mazauna yankin suka fara tattaunawa da gwamnati kan siyan gidajen a ƙarƙashin kwamitin shugaban ƙasa na sayar da kadarorin gwamnati (PIC).
Gwamnatin Tarayya ta sayar da gidajen
Ya kara da cewa a 2021, gwamnatin tarayya ta amince da sayar da wuraren, kuma yawancin mazauna sun biya kuɗin da aka kayyade sannan suka karɓi takardun mallaka.
Sai dai Muhammad Mustapha ya zargi FAAN da kin amincewa da wannan ciniki, duk da cewa gwamnati ta fara aiwatar da manufar sayar da kadarori tun a 2003.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Sabuwar barazana ta tunkaro Sanata Natasha kan zamanta a majalisa
"Rushe gidajen da korar mutane ya zo mana a bazata, saboda haka mun garzaya kotu don neman hana FAAN kutsawa cikin waɗanda yanzu suka zama kadarorin mu.
"Idan FAAN na da wata matsala, ya kamata su tuntubi ma’aikatarsu da kuma fadar shugaban kasa don tabbatar da ingancin takardunmu, wanda kwamitin PIC ya bayar a ƙarƙashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF)", in ji shi.
Dalilin FAAN na fara rusa gidaje a Kano
A nasa martanin, Ahmad Danjuma, mukaddashin babban manajan FAAN na shiyyar Arewa maso Yamma da ke Kano, ya kare matakin rusa gidajen.
Ya ce an gina wuraren ne domin ma’aikatan filin jirgin sama, don haka bai kamata a sayar da su ba ba tare da amincewar hukumar FAAN ba.
A cewarsa, FAAN ba ta da masaniya game da sayar da wuraren har sai da ta ji labari daga jita-jita, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Asali: Original
"An gina waɗannan gidaje fiye da shekaru 35 da suka wuce domin ma’aikatanmu su zauna a kusa da filin jirgin sama don tabbatar da tsaro da ingantaccen aiki.
"Amma sai ga wasu mutane sun tunkari PIC don sayensu a ƙarƙashin manufar sayar da kadarorin gwamnati, ba tare da tuntubar FAAN ba," in ji Danjuma.
Ya jaddada cewa FAAN na aiwatar da umarnin da aka turo mata daga sama domin karɓe kadarorin da kuma dakatar da ci gaba da siyar da su.
Jami'an FAAN na neman cin hanci?
A wani labarin, kun ji cewa hukumar FAAN ta musanta zargin cewa jami'anta na neman cin hanci a filayen jiragen saman Najeriya.
Matar ta wallafa bidiyo tana zargin wasu jami'an FAAN da cin zarafinta tare da neman cin hanci, zargin da hukumar ta ce ba gaskiya ba ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng