Bayan Hukuncin Kotu, Tsohuwar Minista Ta Tarbi Aminu Ado, Sun Yi Buda Baki a Gidanta

Bayan Hukuncin Kotu, Tsohuwar Minista Ta Tarbi Aminu Ado, Sun Yi Buda Baki a Gidanta

  • Tsohuwar minista, Betta Edu ta karɓi bakuncin Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, da tawagarsa domin buda baki a gidanta
  • Mataimakin Gwamnan Jihar Cross River, Rt Hon Peter Odey, da Shugabar Jami’ar Calabar, Farfesa Florence Obi, sun halarci shan ruwan
  • Mambobin Kwamitin Gudanarwa na jami’a, dalibai da sauran al’ummar Musulmi a jihar sun kasance cikin mahalarta a gidan Betta Edu
  • Edu mai shekara 39 ta bayyana taron a matsayin alamar hadin kai da fahimtar juna da gwamnatin Bola Tinubu ke kokarin samarwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Calabar, Cross River - Tsohuwar Ministar jin kai da walwala, Dr. Betta Edu ta karbi bakuncin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Betta Edu ta karbi basaraken a gidanta da ke birnin Calabar domin yin buda baki a daren jiya Laraba 19 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Atiku, El-Rufai, Obi da jiga jigan APC sun hadu domin shirin kifar da Tinubu a 2027

Aminu Ado ya ziyarci gidan tsohuwar minista a Najeriya
Aminu Ado Bayero ya yi buda baki da tsohuwar minista a gwamnatin Bola Tinubu. Hoto: Betta Edu.
Asali: Facebook

Betta Edu ta tarbi Aminu Ado Bayero a gidanta

Wanann na kunshe a cikin wata sanarwa da tsohuwar ministar ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Alhamis 20 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Betta Edu ta ce mataimakin gwamnan jihar da sauran masu ruwa da tsaki sun halarci liyafar da ta shirya a gidanta.

Sanarwar ta ce:

"Na samu damar karɓar bakuncin Mai Martaba, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, CFR, da tawagarsa domin buda baki a gidana da ke Calabar.
"Mataimakin Gwamnan Jihar Cross River, Hon. Peter Odey ya kasance cikin manyan baki da suka halarci wannan taro.
"Shugabar Jami’ar Calabar, Farfesa Florence Obi, ta jagoranci Shugaba da mambobin kwamitin gudanarwa, tare da sauran ma’aikata da ɗaliban jami’ar."
Tsohuwar minista ta karbi bakuncin Aminu Ado a gidanta
Dr. Betta Edu ta taya al'ummar Musulmi murnar Ramadan a ganawarta da Aminu Ado Bayero. Hoto: Betta Edu.
Asali: UGC

Betta Edu ta taya Musulmi murnar azumin Ramadan

Har ila yau, Betta Edu ta ce akwai shugabannin al'ummar Musulmi da sauran mabiya addinin da suka samu damar halartar taron buda bakin a daren jiya.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Ta ce:

"Shugabannin al’ummar Musulmi a Cross River da sauran mabiya addinin Musulunci su ma sun halarci wannan taron buda baki."

Wannan taro ya zo ne a daidai lokacin da Kiristoci ke cikin azuminsu na shekara-shekara wanda ake kira Lent.

Betta Edu ta ce Najeriya ƙasa ce da Allah ya taimaka, musamman ganin yadda shugabancin Bola Ahmed Tinubu ke ƙoƙarin kawo haɗin kai da zaman lafiya.

Daga karshe ta yi wa al'ummar da ke wurin da daukacin mabiya addinin Musulunci murnar azumin Ramadan da kuma murnar cikar Jami’ar Calabar shekaru 50 da kafuwa.

Aminu Ado Bayero ya ziyarci Sarkin Bauchi

A baya, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara jihar Bauchi domin halartar babban taro, tare da nuna godiya ga Sarkin da majalisarsa.

Yayin ganawar, Aminu Ado Bayero ya yi magana kan rigimar sarauta, ya ce jarabawa ce daga Allah kuma ya yi kira ga mutane su ci gaba da addu'a don samun mafita mai alheri.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da 'shugaban riko' na jihar Ribas, bayanai sun fito

Basaraken ya yi addu'ar Allah ya kawar da duk wata matsala, ya kuma gode wa jama'a bisa addu'o'in su da goyon baya ga masarautar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng