Mutane da Dama Sun Mutu da Wata Tanka Ta Yi Bindiga a tsakiyar Jama'a a Abuja

Mutane da Dama Sun Mutu da Wata Tanka Ta Yi Bindiga a tsakiyar Jama'a a Abuja

  • Wata babbar mota ɗauke da gas ta gamu da mummunan hatsari a gadar Karu da ke babban birnin tarayya watau Abuja
  • Rahotanni sun nuna tankar ta fashe a tsakiyar motoci da yammacin ranar Laraba, lamarin da ya sa ake fargabar rasa rayuwa
  • Ganau sun bayyana cewa iftila'in ya faru ne bagatatan kuma ya rutsa da mutane da dama a cikin motoci a birnin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rahotanni sun nuna cewa wata tankar gas ta tarwatse a gadar Karu da ke kan titin Abuja-Nyanya-Keffi a babban birnin tarayya Abuja jiya Laraba 19 ga watan Maris.

Lamarin ya faru ne da yammacin Laraba, inda motoci da dama suka ƙone, wanda ya sa aka fara fargabar yuwuwar asarar rayuka da dama.

Fashewar tanka.
Wata tanka ta fashe a gadar Karu da ke babban birnin tarayya Abuja Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Wata shaidar gani da ido, Fatima Diamond, ta shaida wa jaridar Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar salula cewa iftila'in ya faru ne cikin ƙanƙanin lokaci kuma a tsakiyar jama'a.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki matakin ƙarshe, ya fice daga gidan gwamnatin jihar Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda fashewar tankar ta faru a Abuja

Haka nan, gobarar da ta tashi sakamakon hatsarin babbar mota ta haddasa cunkoso mai tsanani a wannan yanki da ke da yawan zirga-zirgar ababen hawa a Abuja

Fatima Diamond ta ce:

“Abin ya faru cikin ƙankanin lokaci. Motoci da dama sun kone, ni da kaina na kidaya motoci biyar da gobarar ta shafa.
"Amma na ji ana cewa sama da motoci 20 ne suka lalace. Sai da na yi amfani da babur domin tserewa daga wurin.”

Masani kuma mai sharhi kan harkokin yaƙi da ta'addanci, Zagazola Makama ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na X.

Mutane sun shiga firgici da wuta ta kama

Zagazola Makama, ya ruwaito wasu shaidu suna bayyana yadda mutane suka shiga firgici suna gudu domin tsira da rayukansu.

Ya ce mummunan hatsarin ya afku ne yayin da babbar motar dakon kaya mai ɗauke da iskar gas ta samu tangarɗar birki, ta kwacewa direba sannan ta yi kan motoci.

Kara karanta wannan

'Za a iya samun karamin yaki a Rivers,' 'Yan Neja Delta sun gargadi Tinubu

An ruwaito cewa motocin da ke kusa da wurin sun kama da wuta nan take, kuma galibinsu suna ɗauke da fasinjoji.

Abuja.
Ana fargabar rasa rayuwa a wani mummunan hatsarin tanka a Abuja Hoto: Abuja
Asali: UGC

Rahotanni na farko sun nuna cewa babbar motar tana dauke da kwantena cike da iskar gas (CNG) tare da man fetur.

Jami’an agaji, ciki har da ma’aikatan kashe gobara da likitoci, sun garzaya wurin don kokarin shawo kan gobarar tare da taimakon wadanda abin ya shafa.

Ana fargabar mutane da dama sun mutu

Wani wanda ya tsira daga gobarar ya bayyana cewa:

"Na ga motar tana tahowa da gudun tsiya, tana kokarin karkacewa kafin ta bugi wasu motoci. Cikin dan lokaci, sai kuma ta fashe, wuta kuma ta kama ko ina."

Har yanzu ba a tantance yawan wadanda suka rasa rayukansu ba, amma jami’ai na fargabar cewa adadin mutanen da suka mutu ya yi yawa, la’akari da yadda gobarar ta yi tsanani.

Tukunyar gas ta fashe a jihar Kano

Kara karanta wannan

An gano inda Gwamna Fubara yake bayan sojoji sun mamaye fadar gwamnatin Ribas

A wani labarin, kun ji cewa mutum daya ya mutu da wata tukunyar gas ta fashe a unguwar Goron Dutse a jihar Kano.

Bayan fashewar gas ɗin, gobara ta tashi a wasu sassan gidan kafin jami’an agaji su kawo ɗauki don rage asarar da za a samu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng