Dangote zai Gina Tashar Jirgin Ruwa Mafi Girma a Najeriya da Kamfanin Siminti a Ogun

Dangote zai Gina Tashar Jirgin Ruwa Mafi Girma a Najeriya da Kamfanin Siminti a Ogun

  • Aliko Dangote ya bayyana shirin gina tashar jiragen ruwa mafi girma a Najeriya a yankin Olokola, jihar Ogun
  • Haka zalika Dangote zai kuma fadada samar da siminti tare da gina sababbin wuraren samar da siminti a Itori
  • Gwamna Dapo Abiodun ya yaba da shirin, yana mai cewa Ogun za ta zama jagora a samar da siminti a Afirka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Shahararren attajirin Afrika, Aliko Dangote, ya bayyana shirin gina tashar jiragen ruwa da fadada kamfanin siminti a Jihar Ogun.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, da majalisar zartarwarsa a ranar Litinin.

Jihar Ogun
Dangote ya gana da gwamnatin Ogun. Hoto: @DapoAbiodunCON
Asali: Twitter

Gwamnan Ogun ya wallafa a X cewa shirin zai mayar da yankin Olokola cibiyar hada-hadar kasuwanci da bunkasa masana’antu.

Kara karanta wannan

Bututun mai ya fashe a Rivers ana tsaka da zancen tsige gwamna Fubara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote na shirin gina tashar jiragen ruwa

Rahoton Channels TV ya nuna cewa Dangote ya bayyana cewa zai gina tashar jiragen ruwa mafi girma a Najeriya a yankin Olokola.

Aiki zai farfado da shirin da aka dade da watsi da shi a yankin, wanda zai inganta tattalin arzikin Ogun da ma Najeriya baki ɗaya.

Aliko Dangote ya bayyana cewa shirin zai jawo masu zuba jari da kuma inganta harkokin kasuwanci a yankin.

Dangote
Attajirin Afrika, Aliko Dangote. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

A cewarsa, sabuwar tashar jiragen ruwan za ta zama wata babbar hanyar sauƙaƙa fitar da kayayyaki daga Najeriya zuwa kasashen waje.

Dangote zai gina sabon kamfanin siminti

Aliko Dangote ya kuma bayyana cewa ana aikin gina sababbin wuraren samar da siminti guda biyu a Itori da ke Ogun.

Sababbin wuraren za su samar da siminti tan miliyan shida a shekara, wanda zai karawa jihar Ogun ƙarfi a fannin samar da siminti.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Dangote ya tsallake Najeriya, ya shigo da ɗanyen mai daga ƙasar waje

Ya kara da cewa wuraren samar da simintin za su yi aiki tare da tsohon kamfanin siminti da ke Ibeshe wanda ke da ƙarfin samar da tan miliyan 12 a shekara.

Dangote ya bayyana cewa an taba rusa masa masana’antar sau biyu, amma yanzu za a dawo da aikin ne saboda goyon bayan Gwamna Abiodun.

Martanin gwamna Abiodun ga Dangote

Gwamna Dapo Abiodun ya yaba da shirin Dangote, yana mai cewa hakan zai sanya Ogun ta zama jagaba a fannin samar da siminti a Afirka.

Dapo Abiodun ya bayyana cewa cigaban masana’antu irin wannan yana da matukar muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin jihar.

A cewar gwamnan, irin wannan ci gaba zai samar da ayyukan yi ga matasa tare da karfafa bangaren kasuwanci a jihar.

Gwamnan ya kuma jinjina wa Dangote bisa yadda yake tallafawa ci gaban Najeriya ta hanyoyi daban-daban.

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige gwamna ya jefa Shugaba Tinubu a matsala, an yi masa barazana

Ziyartar ginin kamfanin siminti a Itori

Bayan taron, tawagar ta ziyarci wurin da ake aikin samar da sababbin wuraren samar da siminti a Itori.

Haka kuma sun duba titin da ake ginawa karkashin tsarin biyan haraji da gwamnatin tarayya ta amince da shi.

Shugaban gargajiya na Itori, Oba Abdulfatai Akorede Akamo, na daga cikin manyan baki da suka halarci wannan ziyara.

Za a gina kamfanin siminti a Kebbi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da kamfanin siminti a jihar Kebbi.

Gwamnatin jihar Kebbi ta yaba da aikin musamman lura da cewa dubban matasa ne daga jihar da sauran jihohi za su samu aiki a kamfanin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel