El Rufai Ya Tuno Shekaru 8 na Mulkinsa, Ya Fadi Abubuwa 4 da Ya Fi Jin Dadinsu
Kaduna - Bayan komawa jam'iyyar SDP, Mallam Nasir El-Rufai, ya yi magana a kan shekaru takwas da ya shafe a matsayin gwamnan jihar Kaduna.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tsohon gwamnan ya shaida cewa akwai wasu abubuwa akalla hudu da ba zai taba manta da su ba, wadanda ya fi jin dadinsu a shekaru takwas da ya yi a ofis.

Asali: Twitter
A zantawarsa da Freedom Radio Kano, Mallam Nasir El-Rufai ya nuna cewa ko gobe ya sake komawa kan mulki, zai iya maimaita wadannan abubuwa ba tare da da na sani ba.
Abubuwa 4 da El-Rufai ya fi jin dadinsu
1. Ruwan Zaria
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mallam Nasir El-Rufai ya ce duk wani dan asalin karamar hukumar Zaria da ke Kaduna, musamman dan kasa da shekara 40, bai taba ganin ruwan famfo a garin ba.

Kara karanta wannan
'Yadda Ribadu ya hada kai da ICPC domin kai ni kurkuku kafin zaben 2027' - El-Rufai
"To Alhamdulillahi, a kokarinmu, da kokarin wasu da suka assasa harsashi, kamar irinsu Namadi Sambo, muka samar da ruwa a Zaria.
"To amma abin takaici shi ne, shekaran jiya aka aiko mun da bidiyo cewa, an je ana kwance mahadar manyan bututun ruwan da muka jawo ta kan duwatsu a Zaria din."
Tsohon gwamnan ya ce ya ji matukar dadi da samar da ruwa a Zaria, saboda dama aikin gwamnati ana yinsa ne don al'umma.
"A samar da abin da zai rage ciwon jama'a, ya tsarkaka su ga addininsu, babban abu ne. To wannan ya faranta mani rai."
- Nasir El-Rufai.
2. Hanyoyin Kaduna, Zaria da Kafamchan
El-Rufai ya ce abu na biyu da ya fi jin dadinsa shi ne ayyukan titi da suka fadada a kananan hukumomin Kaduna, Zaria da Kafamchan.
Tsohon gwamnan ya ce:
"Kuma na Zaria ya fi faranta mun rai, ba wai don Zaria garinmu ne, ni bazazzagi ne ba, a'a, sai don tun da na tashi ina dan yaro, ba a taba yin wani babban abu da zai sabunta Zaria irin wannan aikin hanyar ba.

Kara karanta wannan
Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu
"Akwai wata hanya wadda ta ratsa Kusfa, wadda aka ce ba zai yiwu a yi hanyar ba, saboda akwai wata kuka, akwai wasu aljanu. Na ce mu ma ai aljanun ne.
"Aka ratsa aka yi hanyar nan. Kuma mun ji dadi, kuma mutanen Zaria sun ji dadi, domin mun basu kudin diyya, wanda wasu da wannan kudin suka sayi gidaje a GRA.
"Shi ya sa ai ko makiyanmu za su ce ai an yi aiki. Kafanchan ma an je an yi aiki. To na ji dadin wannan sosai. Mun yi tsari babba, na yiwa hanyoyi kusan 6,000 kwalta a jihar."
3. Amsa gayyatar Olam
Mallam Nasir ya ce abu na uku da ya fi yi masa dadi, wanda bai shafi biyun da ya lissafa a baya ba, shi ne lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya kira shi, a kan ya rakashi taron UNGA.
"Shekararmu ta farko, a Satumba, shugaba Buhari ya kira ni ya ce yana so in raka shi babban taron majalisar dinkin duniya (UNGA).
"To dai dai lokacin kuma Olam, sun ban katin gayyata, in je Singapore mu tattauna da su, suna so su zuba jari a Kaduna. Sai na je na samu shugaba Buhari.
"Na ce masa ran ka ya dade, na gode, ka sanya ni a cikin tawagarka, amma ka yi hakuri, a daga mun kafa, ga abin da nake so in je in yi. Ina ganin wannan ya fi da in je in raka ka taron UNGA, domin ko na je, ni dan rakiya ne kawai.
"Buhari ya ce 'ahh ka je ka nemi jari, ya fi maka,' sai na ce amma ina roko, a dauki mataimakina, watau marigayi, ya ce ya yarda. Shi ne mataimakin gwamna na farko da aka taba zuwa da shi taron UNGA."
- Nasir El-Rufai.
Tsohon gwamnan ya ce ya amsa gayyatar Olam a watan Satumbar 2015, ya ce zuwa Satumbar 2017, shugaba Buhari ya je Kaduna ya kaddamar da kamfanin Olam.

Kara karanta wannan
Matsalar Obasanjo da Atiku: Kalaman El-Rufai sun ba da mamaki kan rigimarsu a baya
El-Rufai ya kara da cewa:
"Olam ya canja rayuwar manoma a Kaduna. Da masara da waken soya da suke saya kadai, ya sa wannan shekarar Kaduna ta fi ko wace jiha zuwa Haji."
4. Korar malamai sama da 20,000

Asali: Facebook
Mallam Nasir El-Rufai ya ce jihar Kaduna na da makarantun firamare 4,256 a lokacin da ya zama gwamna, amma yawancinsu ba su da kujeru, ban-daki da sauransu.
Tsohon gwamnan ya ce:
"Muka tsaya muka duba, ba za mu iya gyara duk makarantun nan ba, za mu gyara iya wanda za mu iya gyarawa, amma ba nan ne ma matsalar ba.
"Muka ce za mu gyara. Akwai makarantar da ke da dalibai sama da 20,000. Sai da muka gina manyan makarantu uku, sannan aka rarraba su. Sai da muka sayi gidajen mutane, muka biya su diyya, sannna muka gina wadannan makarantu."
Tsohon gwamnan ya ce marigayi Patrick Yakowa, ya ga matsalar malamai a Kaduna, sai ya fito da tsari a shekarar 2012, na cewar an ba malamai lamunin shekara biyar, su je su yo karatun NCE, ko ya kore su zuwa 2017.
A cewar El-Rufai:
"Sai muka samu irin wannan tsarin. Sai muka ce Alhamdulillahi, tun da wani gwamnan ya fara wannan mu za mu karasa. Wadanda ba su da NCE muka ce za mu sallame su.
"Amma kafin nan, sai muka ce, bari mu gwada su, mu yi masu jarabawa. Shi ne a karshe muka kori malaman makaranta fiye da 22,000, mun kuma dauki sababbi, kusan 25,000.
"Wallahi, ni a gani na, babu gudunmawar kirki da muka yi wa jihar Kaduna kamar wannan. Amma ba za a ga sakamakonshi ba sai na da shekara 10, 20."
Tsohon gwamnan na Kaduna ya ce wadannan abubuwa hudu, suna faranta masa rai a duk lokacin da ya tuna da su.
Kalli hira da El-Rufai a nan kasa:
"Uba Sani na karbar 40% na kwangila" - El-Rufai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Malam Nasir El-Rufai ya zargi Gwamna Uba Sani da karɓar kashi 40% daga hannun ‘yan kwangila kafin ba su damar yin aiki a Kaduna.
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta bi wannan tsari ba, kuma hatta shi kansa bai cika haɗuwa da ‘yan kwangilar ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng