Malamai sun rufe kofofin shiga makarantu a Kaduna, El-Rufai ya maida martani

Malamai sun rufe kofofin shiga makarantu a Kaduna, El-Rufai ya maida martani

- Shugabannin makarantun Firamare a jihar Kaduna sun rufe kofofin shiga makarantunsu

- An hana dalibai shiga cikin makarantun

- Gwamna Nasir El-Rufai ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da aikata hakan

- Ya ce dole yaran talakawa a basu ingantatiyar ilimi a Kaduna

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa shugabannin makarantun Firamare a ihar Kaduna sun rufe kofofin shiga makarantunsu.

Haka zalika sun hana dalibai shiga ciki balle har su fara karatu kamar yadda a yau ne aka koma makarantu daga hutun zangon karatu da aka tafi.

Sai dai gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai ya maida martini akan haka.

Malamai sun rufe kofofin shiga makarantu a Kaduna, El-Rufai ya maida martani
Malamai sun rufe kofofin shiga makarantu a Kaduna, El-Rufai ya maida martani

Ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa: “Rahotanni sun kawo cewa wasu shugabannin makarantun Firamare sun rufe kofofin shiga makarantunsu sannan kuma sun hana dalibai shiga ciki.

“Tawagarmu dake lura da hakan sun rigada sun fita sannan kuma muna so mu tabbatarwa da al’umman jihar Kaduna cewa za’a hukunta wadanda suka aikata hakan. Dan Allah idan kun san wani makaranta da aka rufe a safiyar yau, ku sanar dani ta sako kai tsaye tare da sunan shugaban makarantar da kuma sunan makarantar.

“Dole yaran talakawa aa basu ingantatiyar ilimi aa Kaduna!”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng