'Ya Mani Illa': Dangote Ya Fadi Yadda Tsohon Gwamna Ya Rushe Masa Kamfani Sau 2

'Ya Mani Illa': Dangote Ya Fadi Yadda Tsohon Gwamna Ya Rushe Masa Kamfani Sau 2

  • Alhaji Aliko Dangote ya zargi tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun, da rusa masa aikin ginin sabon masana’antar siminti a Itori sau biyu
  • Dangote ya ce sun dawo ci gaba da aikin a jihar Ogun ne saboda manufofin Gwamna Dapo Abiodun da yanayin da ya dace da masu zuba jari
  • Gwamna Abiodun ya bayyana cewa gwamnatin Amosun ta hana ci gaban masana’antar sau uku, ciki har da ginin matatar mai a Legas

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya zargi tsohon gwamna da rushe masa ginin kamfanin siminti.

Aliko Dangote ya zargi tsohon gwamnan Ogun, Sanata Ibikunle Amosun, da rusa masa sabon masana’antar siminti sau biyu a jihar.

Dangote ya koka kan asara da aka jawo masa
Aliko Dangote ya zargi tsohon gwamnan Ogun da jawo masa asara. Hoto: Dangote Group.
Asali: Getty Images

'Yadda tsohon gwamna ya rushe mani kamfani' - Dangote

Kara karanta wannan

Magajin Rafi: Dattijon Arewa ya yi murabus, Masarautar Zazzau ta yi sabon nadi

Sabuwar masana’antar siminti mai layi biyu a Itori, Ewekoro, tana da karfin ton miliyan shida a shekara, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara gina sabon shirin masana’antar Itori ne a ranar 23 ga Disamba, 2023, kuma ana sa ran kammalawa a watan Nuwamba, 2026.

Dangote ya kai ziyara ga Gwamna Dapo Abiodun a Oke-Mosan, Abeokuta, domin duba ci gaban aikin masana’antar da ya kai dala miliyoyi.

Dangote ya ce gwamnatin Amosun ta rushe aikin sau biyu, amma sun dawo saboda irin manufofin gwamnatin Abiodun da ke karfafa masu zuba jari.

Ya ce:

“An rusa masana’antarmu a Itori sau biyu, a karo na biyu har da katangar aka rusa, sai muka bar wurin, amma yanzu mun dawo.”

Gwamna Abiodun ya ce gwamnatin Amosun ta hana ci gaban Dangote sau uku, ciki har da ginin matatar mai da ke Ibeju Lekki, Legas.

Ya ce:

“Sun hana ginin matatar mai, jarin dala biliyan 20, wanda za ta amfani yammacin Najeriya, wannan babban asara ne.”

Kara karanta wannan

'Dan Sule Lamido ya bi sahun mahaifinsa, ya fadi kuskuren ƴan Najeriya a zaben 2023

Gwamna ya ba Dangote tabbacin goyon baya
Gwamna ya gaskata Dangote, ya zargi gwamnatin baya da dakile ci gaba a Ogun. Hoto: Prince Dr. Dapo Abiodun.
Asali: UGC

Gwamna ya fadi asarar da Amosun ya jawo

Gwamna Abiodun ya ce rushewar da aka yi a Itori sau biyu ta na nuna tambaya kan dalilan da ke bayan irin wadannan matakai daga gwamnatin Amosun.

Dangote ya tabbatar cewa idan an kammala masana’antar Itori, jimillar karfin siminti a Ogun zai kai ton miliyan 18 a shekara, cewar Punch.

Ya ce Ogun za ta zama jiha mafi samar da siminti a Afrika, ta fi kowace kasa da yanki a nahiyar wajen yawan samar da siminti.

Dangote ya ce kamfaninsa ne ke kan gaba a Afrika wajen samar da siminti da karfin ton miliyan 52 a shekara a nahiyar.

Ya kara da cewa kashi 70 cikin 100 na simintin ana samar da shi a Najeriya, inda Obajana a Kogi ke da mafi girma da ton miliyan 16.25.

Ya ce masana’antun siminti da takin zamani da suka samar sun sa Najeriya ta dogara da kanta kuma har tana fitarwa don samun kudin waje.

Kara karanta wannan

Hatsabiban 'yan bindiga 18 da aka kashe a 2025 da tasirin hakan ga tsaron Arewa

Dangote ya shigo da mai daga ketare

Kun ji cewa matatar man Aliko Dangote ta sayi ganguna 950,000 na danyen man Ceiba daga Equatorial Guinea, wanda zai iso matatar da ke Najeriya.

An ce sun kamfanin NNPCL ya aika da jiragen ruwa dauke da danyen mai zuwa matatar Dangote domin ci gaba da sarrafawa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel