Tirkashi: Ƴan Majalisa Sun Raba Albashinsu, Sun Miƙawa Tinubu Gudunmawar N705m
- 'Yan majalisar wakilai sun cika alkawarin da suka dauka na bayar da rabin albashinsu don tallafa wa ‘yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali
- A liyafar buda baki da aka shirya a fadar Aso Rock, 'yan majalisar sun mika takardar banki dauke da Naira miliyan 705 ga Shugaba Bola Tinubu
- Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ce gudunmawar ta biyo bayan matakin cire tallafin mai, don rage radadin tsadar rayuwa ga talakawan kasar nan
- Kudin da ‘yan majalisar suka bayar za a rarraba su ga mabukata, domin saukaka halin da mutane ke ciki bayan cire tallafin da Tinubu ya yi a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - 'Yan majalisar wakilai sun cika alkawarin da suka dauka a watannin baya na raba albashinsu gida biyu, tare da bayar da shi matsayin tallafi ga 'yan Najeriya.
Tun a wancan lokacin, 'yan majalisar sun yi alkawarin shafe watanni shida suna karo-karon rabin albashinsu, don ganin kudin sun isa ga mutane masu yawa.

Asali: Twitter
'Yan majalisa sun ba Tinubu rabin albashinsu
Mai ba shugaban kasa shawara kan watsa labarai, Sunday Dare, a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce 'yan majalisar sun cika alkawarinsu a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar Sunday Dare ta ce 'yan majalisar yayin liyafar buda baki a fadar Aso Rock, sun mika takardar kudi ta banki, dauke da Naira miliyan 705 ga shugaba Bola Tinubu.
'Yan majalisar na ganin cewa, Naira miliyan 705, sun yi kaurin da za su iya taimakawa gwamnatin Tinubu wajen ragewa al'umma radadin tsadar rayuwa.
Tinubu ya karbi gudunmawar N705m daga majalisa
Hadimin shugaban kasar, ya bayyana cewa:
"’Yan majalisar wakilai karkashin jagorancin Kakakin majalisa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, sun bada gudunmuwar Naira miliyan 705 ga mabukata a Najeriya.
"Wannan ya cika alkawarin da suka yi na bayar da rabin albashinsu ga mabukata a lokacin rabon tallafin jin ƙai.
"An mika takardar bayar da kudin ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, a lokacin shan ruwa tare da ’yan majalisar wakilai a fadar gwamnati."
'Yan majalisa sun fadi dalilin ba Tinubu N705m

Asali: Twitter
Da yake magana a madadin 'yan majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya bayyana jajircewar majalisar na ganin ta rage radadin wahalar rayuwa da 'yan Najeriya ke fuskanta.
Tajudeen Abbas, ya ce sun yanke shawar bayar da gudunmawar rabin albashinsu a watan Yulin 2024 domin ragewa 'yan Najeriya radadin cire tallafin man fetur.
Ya bayyana cewa, Naira miliyan 705 da suka ba gwamnatin Tinubu gudunmawa za a raba ga 'yan Najeriya mabukata, duk a kokarin tausasa zuciyarsu kan halin da ake ciki.
Kalli bidiyon mika kudin a kasa:
'Yan Najeriya sun dura kan 'yan majalisar wakilai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya sun yi martani bayan 'yan majalisa sun sanar da zabtare rabin albashinsu a matsayin gudunmawa don rage matsin rayuwa a kasar.
Wasu na 'yan Najeriya na ganin cewa alawus din 'yan majalisar ne ya kamata a raba biyu ba wai albashi ba, tun da babu wanda ya san albashin da suke dauka na hakika.
A hannu daya kuma, wasu na zargin cewa 'yan majalisar sun dauki matakin biyo bayan rade-radin fita gangamin zanga-zanga ne, ba wai da kyakkyawan niyya ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng