Gwamna Abba Ya Ɗauko Tsohon Kwamishinan Kwankwaso, Ya Naɗa Shi a Muƙami

Gwamna Abba Ya Ɗauko Tsohon Kwamishinan Kwankwaso, Ya Naɗa Shi a Muƙami

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin sabon kwamishinan gidaje na Kano a ranar Litinin
  • Kafin naɗinsa, Ibrahim ya kasance shugaban hukumar (KNUPDA), inda ya taka rawa a wajen gina manyan biranen jihar Kano
  • Gwamna Abba ya yabawa Ibrahim Adamu bisa rawar da ya taka wajen raya biranen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo
  • An buƙaci sabon kwamishinan da ya magance matsalar gidaje a Kano, tare da haɗa kai da cibiyoyi don samar da gidaje masu sauƙi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin sabon kwamishinan raya gidaje na jihar.

An gudanar da bikin rantsar da sabon kwamishinan ne a ranar Litinin, inda Antoni Janar na Kano, Haruna Isah Dederi, ya jagoranci rantsuwar.

Kara karanta wannan

Abin da Abba Kabir ya fadawa malamai da ya faranta musu rai yayin buda baki a Kano

Gwamnan Kano, Abba ya yi magana yayin da ya nada sabon kwamishinan raya gidaje
Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya rantsar da sabon kwamishinan raya gidaje. Hoto: Abba Muhammad Tukur
Asali: Facebook

An nada sabon kwamishinan gidajen Kano

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da sanarwar rantsuwar a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce kafin nadin Arch. Ibrahim Adamu a matsayin kwamishinan gidaje, ya kasance shugaban hukumar tsara birane da raya Kano (KNUPDA).

Gwamna Abba Yusuf ya yaba wa Ibrahim Adamu bisa kwazonsa da gudunmawar da ya bayar wajen raya yankunan birane na jihar Kano.

Inda Gwamna Abba ya hadu da Ibrahim

Ya tunatar da irin rawar da sabon kwamishinan ya taka a tsarawa da gina rukunin gidajen Kwankwasiyya, Amana, da Bandirawo tsakanin 2013 da 2015.

Sanarwar ta rahoto Gwamna Abba yana cewa:

"Arch. Ibrahim Yakubu Adamu na daya daga cikin kwararrun masu tsara gine-gine da muka taɓa samu a Kano. Na fara haɗuwa da shi a lokacin hidimar NYSC a Abuja, kuma kwarewarsa ta burge ni.

Kara karanta wannan

Mene ake kitsawa?: Barau ya gana da Baffa Bichi da tsohon kwamishinan Abba

"A wancan lokaci, a matsayina na shugaban hukumar shirye-shiryen ilimi da gudanarwa a Ogun, na ba shi aikin tsara gine-gine na cibiyar, kuma ya zarce tsammanina."

Ibrahim ya taba rike mukamin kwamishina a Kano

Gwamna Abba ya yi magana da ya nada Arch. Ibrahim a matsayin kwamishinan Kano
Arch. Ibrahim Adamu ya taba rike kwamishina a lokacin mulkin Kwankwaso. Hoto: Abba Muhammad Tukur
Asali: Facebook

Gwamna Yusuf ya tuna cewa Ibrahim Adamu ya rike mukamin kwamishinan ayyuka da gidaje daga 2011 zuwa 2015, inda ya jagoranci manyan ayyuka.

"Adamu ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa biranen Kwankwasiyya, Amana, da Bandirawo. Lokacin da na hau mulki a matsayin gwamna, na naɗa shi shugaban KNUPDA, inda ya yi aiki tukuru.
"Ya dace a ce yanzu ya ɗauki babbar nauyi a matsayin kwamishina."

- Inji Gwamna Abba Yusuf.

Gwamnan ya bukaci sabon kwamishinan da ya tunkari matsalar gidaje a Kano, musamman ga ma’aikatan gwamnati.

Ya bukace shi da yin hadin gwiwa da cibiyoyin hada-hadar kudi da masu ruwa da tsaki don bunkasa gidaje masu saukin kudi a jihar.

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige gwamna ya jefa Shugaba Tinubu a matsala, an yi masa barazana

Abba ya nada kwamishinan tsaron Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Kano ya naɗa Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris a matsayin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana naɗin ne yayin rantsar da sababbin 'yan majalisun gudanarwa na jami’o’i da manyan makarantu a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel