Gwamnatin Abba Ta Kawo Sabon Tsarin Biyan Albashi, An Aika Sako ga Ma'aikatan Kano
- Gwamnatin Kano ta umarci ma’aikatan jihar da su tantance albashinsu na watan Maris domin magance kura-kuran da aka samu a baya
- Sakataren gwamnatin jihar ya ce za a lika jerin albashin kowanne ma’aikaci don saukaka tantancewar, kafin gwamnati ta fara biyansu
- Gwamnati ta kafa kwamitin tantance albashi karkashin jagorancin shugaban ma’aikata, domin tabbatar da an biya albashi kafin Sallah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnatin jihar Kano ta umarci duk ma’aikatan gwamnati da su tantance albashinsu na watan Maris kafin a biya su, domin kauce wa kura-kurai.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ibrahim Faruk, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa a ranar Litinin.

Asali: Twitter
Gwamnatin Kano ta kawo tsarin biyan albashi
Alhaji Ibrahim ya ce an dauki matakin ne bayan korafe-korafen zabtare kudade daga albashin ma’aikata a watannin Janairu da Fabrairu, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Don saukaka tantancewar, za a lika bayanin albashin ma’aikata a wurare masu muhimmanci a ma’aikatun gwamnati da sakateriyoyin kananan hukumomi 44 na jihar.
Ya ce:
"Za a manna jerin albashin ma’aikata a wurare masu muhimmanci da ke a harabar ma’aikatun gwamnati da sakatariyoyin kananan hukumomi 44 a jihar don saukaka tsarin tantancewar."
Sakataren gwamnan ya ce ma’aikata za su duba bayanin albashin da aka lika don tabbatar da sunayensu da adadin albashin da aka sanya musu.
An fadawa ma'aikata amfanin tantance albashinsu
Ya ce wanda ya ga tasgaro a albashinsa zai iya kai rahoto ga ma’aikatarsa ko hukumar da yake aiki a ciki domin a gyara kuskuren da wuri.
“Duk wani ma’aikacin gwamnati da ke da korafi ya garzaya zuwa ma’aikata, sashe, ko hukumar da yake aiki domin tantance albashinsa kuma ya kai rahoton duk wani kuskure da aka samu domin a dauki matakin gaggawa.”

Kara karanta wannan
Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu
- Inji Alhaji Ibrahim Faruk.
Domin tabbatar da ingantaccen tantancewar, gwamnati ta kafa kwamiti karkashin jagorancin shugaban ma’aikata, Alhaji Abdullahi Musa.
Alhaji Faruk ya bayyana cewa an umarci kwamitin da ya kammala aikin cikin gaggawa domin a biya albashin watan Maris a kan kari.
Ya tabbatar wa ma’aikata cewa wannan aiki ba zai kawo cikas ga ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin jihar Kano ba.
Gwamnatin Kano za ta biya albashi kafin Sallah

Asali: Twitter
New Telegraph ta rahoto cewa gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa an biya albashin kafin bukukuwan Sallah, domin ma'aikata su yi walwala.
Sakataren gwamnatin ya kuma jaddada cewa gwamnati ba ta manta da bukatar ma’aikata na samun albashinsu kafin bikin karamar Sallah ba.
Ya na mai cewa:
"Gwamnati na sane da gabatowar bukukuwan karamar Sallah da kuma muhimmancin biyan albashin watan Maris kafin ranar bikin."

Kara karanta wannan
Albashi N500,000: 'Yan kasar Sin suka shigo Najeriya, sun kafa kamfanin sarrafa lithium a Nasarawa
Ya bukaci duk ma’aikatan da su dauki wannan tantancewa da muhimmanci domin guje wa duk wata matsala da ka iya shafar biyan albashinsu.
Abba ya dakatar da shugaban ma'aikata
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da mukaddashin shugaban ma’aikata bisa zargin hannu a batun albashin ma’aikata.
An nada Malam Umar Muhammad Jalo a matsayin sabon mukaddashin shugaban ma’aikatan gwamnati yayin da ake gudanar da bincike.
Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa duk wanda aka kama da zabtare albashin ma’aikata zai fuskanci hukunci ba tare da nuna sani ko bambanci ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng