Kano: Ma'aikatan gwamnati sun yi sallah ba albashi, sun caccaki Ganduje

Kano: Ma'aikatan gwamnati sun yi sallah ba albashi, sun caccaki Ganduje

  • Ma'aikatan Kano sun caccaki Gwamna Ganduje, saboda yadda aka gaza biyansu albashn watan Afirilu don samun damar gudanar da shagalin bikin sallah
  • Ma'aikatan sun zargi Ganduje da nuna halin ko in kula da bukatunsu, tare da mayar da su mabaratan karfi da yaji ga abokanai da danginsu
  • A cewarsu, abun da ya fi damunsu shine yadda gwamnan ya yi tafiyarsa kasar Saudi ba tare da bayyana musu dalilin jinkirin albashin ba

Kano - Ma'aikatan gwamnati na jihar Kano sun caccaki gwamnatin jihar saboda yadda ta gaza biyansu albashin watan Afirilu, wanda suka ce ya kuntata shagalin bikin karamar sallah a jihar.

Ma'aikatan gwamnatin sun taya musulman fadin duniya murnar bikin karamar sallar a ranar Litinin - Wanda ke bayyana kammala azumin kwanaki 30 na watan Ramadana.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tambuwal ya gana da malaman Islama kan batun dalibar da ta zagi Annabi

Kano: Ma'aikatan gwamnati sun yi sallah ba albashi, sun caccaki Ganduje
Kano: Ma'aikatan gwamnati sun yi sallah ba albashi, sun caccaki Ganduje. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ma'aikatan sun zargi gwamna Abdullahi Umar Ganduje da nuna halin ko in kula da damuwarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ma'aikacin gwamnati, wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda tsaron ko ta kwana, ya ce gwamnan ya maida su "Cikakkun mabarata, wadanda ke maulatar kudi daga abokanai da danginsu don biya wa kawunansu bukatu."
"Ba a biyamu albashin watan Afirilu ba, halin da muke ciki abun damuwa ne. Misali, idan na gaza samar da abinci ga matata da 'ya'yana," a cewar ma'aikacin gwamnatin.
"Na san wani abokin aikina, wanda bai samu komai ba bayan kaskantar da kansa da ya yi wurin rokon mutane kudi.
"Na ji labarin cewa gwamnan (Ganduje) na kasar Saudi Arabiya yana ibadah, ba tare da dubi da damuwar ma'akatansa ba, wanda shi kansa yana da tarin 'ya'yan da ya kamata ya kula da su a shagalin bikin sallar nan," ma'aikacin gwamnatin ya kara da fadin.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Wani ma'aikacin gwamnatin, mazaunin gundumar Fagge cikin birinin Kano, ya bayyanawa Premium Times yadda yunwa ke kokarin halaka ma'aikata.

"Ba abu bane mai sauki gare mu. Bikin sallar bai mana dadi ba," ma'aikacin cikin halin damuwa ya fadi hakan. Ya bayyana yadda ya gaza dinkawa 'ya'yansa kayan sallah.

Ya ce abun bakinciki game da jinkirin biyan albashin shi ne yadda gwamnatin ba ta sanarwa da ma'aikata dalilin rashin biyansu albashi ba.

Kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba, bai amsa kiraye-kiraye da sakonnin waya ba, yayin da aka bukaci tsokaci daga gare shi.

Haka zalika, ba a sami wayar shugaban kungiyar kwadago ta jihar (NLC), Kabir Minjibir, a nan take don jin ta bakinsa ba.

Kano: Ganduje ya haramta zuwa da fostoci masallatan idi ko wurin shagulgulan sallah

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya haramta yawo da manyan fostoci da kanana yayin sallar Idi da sauran shagulgulan sallah, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Iftila'i: An tafka ruwan sama a Damaturu, ya rusa gidaje, ya hallaka mutane 5

A sakon sallanshi da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar a wata takarda, gwamnan ya ce hakan zai iya kawar da hankali daga sallah.

"Yayin da ake ganinsu bauta mai matukar muhimmanci bayan tsawon lokacin da aka dauka ana azumin Ramadana, inda shagulgulan al'adu ke biyo baya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel