Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara bayan Sun Gwabza da 'Yan Ta'addan ISWAP
- Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasara kan ƴan ta'addan ISWAP a jihar Borno
- Sojojin na haɗin gwiwa sun yi nasarar daƙile hare-haren da ƴan ta'addan suka kai a wani sansaninsu da ke ƙaramar hukumar Bama
- Jami'an tsaron sun yi gumurzu da ƴan ta'addan, inda suka fatattake su zuwa daji ba tare da an samu asarar rai daga ɓangarensu ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun haɗin gwiwa a ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar daƙile harin ta’addanci na ƴan ta'addan ISWAP a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun daƙile harin da ƴan ta'addan suka kai a sansaninsu na Mayanti, da ke Banki a ƙaramar hukumar Bama, jihar Borno.

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka daƙile harin ƴan ISWAP
Majiyoyi sun bayyana cewa cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 01:15 na daren ranar Lahadi, 16 ga watan Maris 2025.
Dakarun sojojin sun fuskanci ƴan ta’addan inda suka yi musayar wuta, lamarin da ya tilasta musu janyewa. Babu asarar rai daga ɓangaren sojojin.
Daga bisani, da misalin ƙarfe 02:03, wata tawagar sojoji da aka turo, ta fuskanci harin kwanton ɓauna daga ƴan ta’addan Boko Haram/ISWAP a kan hanyar Banki Junction-Mayanti.
Ƴan ta’addan sun dasa abubuwan fashewa guda biyu a hanyar domin hana sojojin wucewa.
Rundunar da aka turo ƙarƙashin jagorancin kwamandanta, ta gaggauta mayar da martani, inda suka fatattaki ƴan ta’addan, tare da tilasta musu tserewa.
A yayin gumurzun, wasu sojojin Najeriya guda biyu sun samu raunuka.
Sojoji sun taso ƴan ta'adda a gaba
Sojojin Operation Hadin Kai na nuna jajircewa da ƙwarewa wajen daƙile hare-haren ƴan ta’adda, lamarin da ke ci gaba da ragewa ISWAP damar aiwatar da munanan ayyukansu a yankin Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe mahaddacin Kur'anin da suka sace a Katsina? An gano gaskiya
Wannan farmaki ya ƙara tabbatar da irin nasarorin da dakarun ke samu wajen hana ƴan ta’adda sakat da kuma tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da matsalar tsaro.
Sojoji na ci gaba da sintiri da bincike a yankin domin kawar da sauran barazanar da ƴan ta'addan za su iya kawowa.
Ayyukan haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da kuma rahotannin sirri suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa yankin ya samu dawowar kwanciyar hankali.
Jami'an Sojoji sun daƙile harin ƴan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun kawo cikas ga wani yunƙurin kai hari da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi a jihar Adamawa.
Dakarun sojojin sun yi nasarar daƙile harin na ƴan ta'addan ne a garin Garkida da ke ƙaramar hukumar Gombi ta jihar.
Ƴan ta'addan dai sun yi yunƙurin kai farmaki ne a wani shingen bincike na jami'an tsaron da ke a garin na Garkida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng