Gwamnoni Sun Fara Lallaba Gwamnati, Ana Son Hana Kananan Hukumomi Kudinsu

Gwamnoni Sun Fara Lallaba Gwamnati, Ana Son Hana Kananan Hukumomi Kudinsu

  • Gwamnonin jihohin sun fara daukar matakai don dakile yunkurin biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye daga CBN zuwa kananan hukumomi
  • Gwamnonin sun yi amfani da damar liyafar bude baki don tattaunawa da Bola Tinubu kan batun kudin kananan hukumomi bayan hukuncin kotun koli
  • Majiya daga fadar gwamnatin tarayya ta bayyana cewa gwamnoni sun fi son a aika kudin ga asusun jihohi domin biyan wasu basussuka da ke gabansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnonin jihohi sun kaddamar da sabon yunkuri don dakile shirin rarraba kudin tarayya kai tsaye ga kananan hukumomi.

Wannan na zuwa ne a wani sabon kokari na jan kafa wajen aiwatar da hukuncin Kotun Koli kan ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Sanusi vs Aminu Ado: An gargadi Abba Kabir da sauran hukumomi bayan hukuncin kotu

Gwamnati
Gwamnoni na son a hana kananan hukumomi kudadensu kai tsyae Hoto: @Official BAT
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa wasu daga cikin gwamnonin sun nuna rashin amincewarsu da CBN ta rika biyan kudin kananan hukumomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin sun bayar da hujjar cewa akwai bukatar warware bashin biliyoyin Daloli da ake zargin kananan hukumomi sun tarawa kansu.

Albashin kananan hukumomi: Gwamnoni sun lallabi Tinubu

The Cable ta wallafa cewa wasu jami’an fadar shugaban kasa sun bayyana cewa gwamnonin sun yi amfani da damar liyafar bude baki don jawo hankalin Shugaba Tinubu batun.

Haka kuma sun ja hankalinsa wajen ci gaba da tattaunawa kan batun rarraba kudaden kai tsaye ga kananan hukumomi, wanda ya sha cikas.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce:

“Lokacin da gwamnonin suka zo Iftar a ranar Litinin, sun nemi su gana da shugaban kasa, wanda aka yi a ranar Talata.
Wasu daga cikin gwamnonin sun gana da shugaban kasa. Sun kwashe dogon lokaci tare da shi. Sun bar Fadar Gwamnati bayan karfe 6:00 na yamma.”

Kara karanta wannan

Jami'an tsaron Kano sun dira kan masu kunnen kashi, an cafke matasa 28

Gwamnoni na son kudin kananan hukumomi

Wata majiya da ta san yadda tattaunawar tsakanin Tinubu da gwamnonin ta kasance ta bayyana cewa gwamnonin sun so a rika tura kudaden ne zuwa asusunsu ba na kananan hukumomi ba.

Majiyar ta ce:

“Abubuwa biyu ke faruwa. Gwamnatin tarayya na so a biya kudin zuwa CBN, kuma a buɗe asusun ajiyar dukkan kananan hukumomi a CBN.
“Amma gwamnonin suka ce a’a, ba su yarda da haka ba. Sun ce idan aka tura kudaden zuwa CBN, hakan na nufin har yanzu gwamnatin tarayya ce ke da iko da su gaba daya.”
Tinubu
Gwamnoni sun gana da Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Majiyar ta kara da cewa:

“Daya daga cikin gwamnonin ya ce idan CBN ne ke kula da asusun, sai an samu amincewar Akanta-Janar kafin a cire kudin.
Wannan na nufin kudin har yanzu su na hannun gwamnatin tarayya, kuma ba su so hakan. Su na so a tura kudaden kai tsaye zuwa bankunan kasuwanci. Amma gwamnatin tarayya ta ce a’a.”

Kara karanta wannan

Bayan sauya shekar El Rufa'i, Tinubu ya ba gwamnoni da ministoci umarni

Kotu ta yanke hukunci kan kananan hukumomi

A wani labarin, kun ji cewa babban kotun jiha karkashin Mai shari’a Musa Ibrahim Karaye ta yanke hukunci kan rikicin kudin kananan hukumomi 44 na jihar da APC ke son a hana su.

Dambarwar ta fara ne bayan APC ta shigar da kara, tana neman kotu ta dakatar da tura kudun kananan hukumomin Kano kan zargin an yi zaben shugabannin ba bisa ka'ida ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel