'Dan Gwamna Bala Mohammed Ya Gargadi Seyi Tinubu kan Raba Abinci a Bauchi
- Shamsuddeen Bala Mohammed ya bukaci Seyi Tinubu ya tallafa wa matasan Bauchi da ayyukan yi da jari maimakon raba abinci
- 'Dan gwamnan ya ce matasan Bauchi suna bukatar horo a fannin sana'o'i da fasahar zamani, ciki har da cinikayyar kirifto don dogaro da kansu
- Seyi Tinubu yana rangadi jihohin Arewa inda ake ganin yana raba abinci ga mutane a lokacin buda baki a watan azumi da ake ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Dan gwamnan Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed, ya yi kira ga Seyi Tinubu da ya yi amfani da ziyararsa don tallafa wa matasan jihar.
Shamsuddeen Bala Mohammed ya ce bai kamata a mayar da matasan Bauchi kamar masu bara ba, sai dai a basu damar dogaro da kansu ta hanyar ayyukan yi da horo na musamman.

Kara karanta wannan
"An takura wa shugaban kasa" Seyi Tinubu ya kare mahaifinsa daga sukar 'yan adawa

Asali: Facebook
Legit ta gano bayanin da Shamsudden Bala Mohammed ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Punch ta ruwaito cewa dan gwamnan ya yi magana ne yayin da Seyi Tinubu ke rangadi jihohin Arewa, inda ake ganin yana raba kayan abinci ga al’umma a lokacin buda baki.
Yayin da Seyi Tinubu ya fara shiga Arewa maso Gabas, ana sa ran zai iya shiga jihar Bauchi domin ziyarar a kowane lokaci daga yanzu.
Bukatar tallafin dogaro da kai a Bauchi
Shamsuddeen Bala Mohammed ya bayyana cewa cewa matasan Bauchi suna bukatar ayyukan yi da jari, ba kayan abinci kawai ba.
Ya bukaci a basu tallafi kamar Keke NAPEP, kudin kafa kasuwanci, da kuma horo a fannin ICT da cinikayyar kirifto don inganta rayuwarsu.
Shamsudden Bala Mohammed ya ce hakan zai taimaka wajen rage zaman banza da inganta rayuwar al'umma a jihar.

Kara karanta wannan
"Manufofinsa na amfanar kowa," Tanko Yakasai ya nemi Arewa ta mara wa Tinubu baya
Abinci zai kare rana daya - Shamsudden
Shamsuddeen ya ce yana da kyau a koya wa matasa yadda za su dogara da kansu fiye da basu abinci da zai kare a rana ɗaya.
Ya ce bai dace a raba abinci ga matasan Bauchi ba wanda hakan zai mayar da su kamar mabarata masu bukata.
A cewar Shamsudden, matasan Bauchi suna da ƙwazon da zai iya amfani wa ƙasa baki ɗaya idan aka ba su horo maimakon abinci.

Asali: Facebook
Seyi Tinubu na raba abinci a Arewa
A yayin ziyarar da yake yi a jihohin Arewa, Seyi Tinubu ya raba abinci ga mutane a Kano, Kaduna, Yobe da wasu jihohi.
Akwai ra’ayoyi masu karo da juna kan irin wannan tallafi, inda wasu ke ganin ya kamata a fi mayar da hankali kan samar da ayyukan yi.
A yanzu haka dai kallo ya koma kan dan shugaban kasar domin ganin abin da zai gabatar idan ya shiga jihar Bauchi.

Kara karanta wannan
Abin da Abba Kabir ya fadawa malamai da ya faranta musu rai yayin buda baki a Kano
Seyi Tinubu da takara a Legas
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan siyasa sun fara kira da cewa ya kamata dan Bola Tinubu ya nemi takarar gwamnan a jihar Legas.
Masu maganar sun ce lokaci ya yi da Seyi Bola Tinubu zai tsaya takara, kuma da ma a cewar masu maganar, kyan da ya gaji ubansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng