"An Takura wa Shugaban Kasa" Seyi Tinubu Ya Kare Mahaifinsa daga Sukar 'Yan Adawa

"An Takura wa Shugaban Kasa" Seyi Tinubu Ya Kare Mahaifinsa daga Sukar 'Yan Adawa

  • Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya dira a kan wasu 'yan siyasa bisa zargin cewa sun saka gwamnatin tarayya da iyalansu a gaba
  • A rangadin wasu daga cikin jihohin Arewa da Seyi Tinubu ke yi, ya bayyana cewa wadannan mutane sun tashi daga turbar sukar siyasa
  • Seyi Tinubu ya bugi kirji a kan salon mulkin mahaifinsa, inda ya bayyana cewa ya fi kowane shugaban kasa a Najeriya iya tafiyar da kasar
  • Ya kara nanata wasu daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Bola Tinubu ta ke y wa 'yan Najeriya, musamman ta fuskar tattalin arziki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar AdamawaSeyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, ya ce wasu mutane ba su daina kai wa mahaifinsa da iyalansa farmaki a kan matsalolin Najeriya ba.

Kara karanta wannan

'Gwanda Buhari': Shugaban jam'iyya ya fadi azabar da ake sha a mulkin Tinubu

Yayin da yake magana da wasu matasa a Yola, a jihar Adamawa Seyi ya bayyana mahaifinsa a matsayin shugaban ƙasa mafi girma a tarihin Najeriya.

Tinubu
Seyi Tinubu ya kare mahaifinsa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Cable, ta ruwaito cewa tun farkon shekarar nan, ɗan shugaban ƙasar ya fara rangadin jihohin Arewa da Kudancin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin rangadin, Seyi Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi da manyan ’yan siyasa da ke shiyyar tare da gana wa da wasu matasan ‘yan siyasa a yankin.

Seyi ya fadi matsayar gwamnatin Tinubu

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Seyi Tinubu ya ce duk da hare-haren da ake kai wa mahaifinsa, shugaban kasa ya kuduri aniyar inganta Najeriya.

Ya ce:

“Ba siyasa ba ne, amma suna ci gaba da kawo hari a kaina, suna kawo hari a kan iyalina, suna kawo hari a kan mahaifinmu, suna kawo hari a kan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shugaban ƙasa mafi kwazo a tarihin Najeriya.”

Kara karanta wannan

Dan gwamna Bala Mohammed ya gargadi Seyi Tinubu kan raba abinci a Bauchi

"Shi ne kawai shugaban ƙasa da ya sa mutanenku sun zauna a gida, shugaban ƙasa ɗaya tilo da ke kula da matasa, kuma shi ne shugaban da ya ƙirƙiri wani dandalin da matasa za su samu dama su yi fice."

"Tinubu ya inganta tattalin arziki" — Seyi

Seyi Tinubu ya bayyana cewa mahaifinsa ne shugaba daya tilo da ya tsaya tsayin daka wajen farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya.

Tinubu
Seyi Tinubu ya caccaki wasu 'yan siyasa Hoto: Aso Villa
Asali: Facebook

Ya ce:

"Shi ne shugaban kasar da ya ƙirƙiri tattalin arziki da kowa ke amfana da shi, shugaban da ba ya ƙoƙarin tara wa kansa dukiya."
Duk da haka, an yi wa Seyi Tinubu suka kan yadda yake raba tallafi a yankin Kudu maso Yamma, amma a Arewa ya takaita kan bayar da gudummawa kaɗan.

Yakasai ya yabi manufofin Tinubu

A baya, mun wallafa cewa dattijon dan siyasa, Alhaji Tanko Yakasai ya shawarci mazauna Arewacin Najeriya da su ci gaba da mara wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu don ci gaban kasa.

Kara karanta wannan

"Manufofinsa na amfanar kowa," Tanko Yakasai ya nemi Arewa ta mara wa Tinubu baya

Alhaji Tanko Yakasai, wanda guda ne daga cikin manyan magoya bayan shugabancin Bola Tinubu, ya kara da cewa akwai tanadin da gwamnatin tarayya ta yi wa 'yan Najeriya, musamman Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel