Obasanjo Ya Dawo da Maganar Karin Albashi, Ya Ce N70,000 Ta Yi Kadan

Obasanjo Ya Dawo da Maganar Karin Albashi, Ya Ce N70,000 Ta Yi Kadan

  • Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce sabon mafi karancin albashi ba zai isa biyan bukatun ma’aikata ba
  • Olusegun Obasanjo ya zargi shugabannin kungiyoyin kwadago da fifita bukatun kansu fiye da muradun ma’aikata
  • Bayan haka, Obasanjo ya yi zargin cewa tun daga 2015 ake rufe wa shugabannin kwadago baki da kudi masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya caccaki sabon mafi karancin albashi na N70,000 da shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu.

Olusegun Obasanjo ya yi sukar ne yana mai cewa hakan bai wadatar wa ma’aikata biyan bukatunsu na yau da kullum.

Obasanjo
Obasanjo ya ce albashin N70,000 ya yi kadan. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Punch ta wallafa cewa Obasanjo ya fadi haka ne a sabon littafinsa mai suna Nigeria: Past and Future, a nan ya ce sabon albashin bai isa a biya kudin sufuri, abinci, da muhalli ba.

Kara karanta wannan

'Yan jagaliya aka tara': Obasanjo ya fadi halayen sarakuna da ake nadawa a yanzu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma zargi shugabannin kungiyoyin kwadago da cin amanar ma’aikata ta hanyar fifita muradun kansu maimakon kare hakkin wadanda suka zabe su.

Maganar shiga siyasar 'yan kwadago

A cikin babi na 17 na littafinsa, Obasanjo ya zargi shugabannin kwadago da amfani da mukamansu wajen cimma burin siyasa, maimakon kare muradun ma’aikata.

Daily Post ta wallafa cewa Obasanjo ya ce:

“Shin ta yaya shugaba a kungiyar kwadago zai kasance yana shirin zama dan takarar gwamna tun yana kan mukaminsa?
"Saboda irin wadannan burikan siyasa, yawancin shugabannin kungiyoyin kwadago sun kasa yin aikin da ya dace."

Obasanjo ya ci gaba da cewa:

“Ma’aikata suna wahala, amma shugabanninsu suna neman matsayi a siyasa.
"A lokacin tattaunawa, sai su yi barazanar tafiya yajin aiki, daga baya sai a shigar da su daki a cika hannayensu da kudi, su kuma su yi shiru.”

Tsohon shugaban kasar ya ce tun daga 2015 ake wannan al’amari, kuma maimakon ya ragu, sai kara tabarbarewa yake yi.

Kara karanta wannan

Rashawa: Obasanjo ya nemi kwacewa Buhari zani a kasuwa, Malami ya kare kansa

Shugaban NLC
Shugaban 'yan kwadagon Najeriya yayin zanga zanga. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Yadda aka yi karin albashi a Najeriya

A ranar 29 ga Yuli, 2024, Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 bayan tattaunawa da kungiyoyin kwadago.

Tun da farko, kungiyoyin kwadago sun bukaci N250,000 a matsayin mafi karancin albashi, amma daga karshe gwamnati ta amince da N70,000 kacal.

Kafin hakan, mafi karancin albashi a Najeriya yana kan N33,000, wanda tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a ranar 18 ga Afrilu, 2019.

Obasanjo ya na so a hana 'yan kwadago siyasa

Tsohon shugaban kasar ya kuma caccaki jami’an gwamnati da ke ikirarin cewa suna biyan shugabannin kwadago kudi domin su daina yajin aiki.

Ya ce:

“Ta yaya wani babban jami’i da ke kusa da shugaban kasa zai ce, ‘Mun biya su su daina koke-koke’?
"Da me irin wadannan shugabannin kwadagon ke amfanar kasar nan?”

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige gwamna ya jefa Shugaba Tinubu a matsala, an yi masa barazana

Daga karshe, Obasanjo ya bayar da shawarar kafa doka da za ta tilasta shugabannin kwadago su jira a kalla shekaru biyar bayan barin mukamansu kafin su shiga harkokin siyasa.

Obasanjo ya zargi Buhari, Tinubu da rashawa

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya zargi Muhammadu Buhari da Bola Tinubu da rashawa.

Obasanjo ya ce a shekaru takwas da Buhari ya yi an samu gagarumin cin hanci kuma Bola Tinubu ma ya daura daga inda ya tsaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng