Jami'an Tsaro Sun Samu Nasara, Sun Ragargaji Gawurtattun Ƴan Bindiga a Katsina

Jami'an Tsaro Sun Samu Nasara, Sun Ragargaji Gawurtattun Ƴan Bindiga a Katsina

  • Jami’an tsaro sun dakile harin ‘yan bindiga a garin Dan Takuri, da ke Katsina, bayan samun sahihan bayanai daga DSS kan shirin farmakin
  • An samu musayar wuta mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindigar, wanda ya kai ga kashe dan ta'adda daya, yayin da sauran suka tsere
  • An kwato bindigar AK-47, babur, da miyagun kwayoyi, yayin da aka bukaci jama’a su bada rahoton duk wanda suka gani da raunukan harsashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Dakarun hadin gwiwar jami’an tsaro sun samu nasarar dakile harin ‘yan bindiga a garin Dan Takuri, da ke karamar hukumar Danmusa, jihar Katsina.

An rahoto cewa, jami’an da suka halarci farmakin sun hada da ‘yan sanda, jami'an tsaron farar kaya (DSS), da dakarun tsaron Katsina (KSCWC).

Rahoto ya yi bayanin kokarin jami'an tsaro na dakile harin 'yan bindiga a Katsina
Jami'an tsaro sun dakile harin masu garkuwa da mutane a wani kauyen Katsina. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jami'an tsaro sun samu bayanai kan 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

An gudanar da samamen ne ranar 15 ga watan Maris, da misalin karfe 12:30 na rana, bayan samun sahihan bayanai daga DSS, inji rahoton Zagazola Makama a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan sirri sun nuna cewa ‘yan bindiga sun taru a yankin Dutsen Maijele domin kaddamar da farmaki kan al’ummar yankin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce an samu bayanai da ke nuna cewa ‘yan bindigar sun hallara yankin dauke da mugayen makamai.

Katsina: Jami'an tsaro sun fafata da 'yan bindiga

Shugaban ofishin 'yan sanda na garin Danmusa, ya jagoranci kai farmakin cikin gaggawa, tare da hadin gwiwar jami’an KSCWC da DSS.

Rahoton ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun yi artabu da ‘yan bindiga a wurin, wanda aka dauki lokaci ana mummunar musayar wuta.

Bayan kura ta lafa, rahoton ya ce an kashe dan bindiga daya, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Zamfara: An hallaka hatsabibin ɗan ta'adda da aka daɗe ana nema ruwa a jallo

Jami'an tsaro sun kwato makaman 'yan bindigar

Bayan fafatawar, jami’an tsaro sun bincike wurin domin kwato makamai da kayan aikinsu, inda suka kwato bindigar AK-47 mai harsasai uku, tare da babur din Boxer maras rijista.

Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da tabar wiwi 50, da kuma lemukan kara kuzari 32. Sannan an kwato wasu miyagun kwayoyi, adduna, da kayayyaki masu hadari.

Jami’an tsaro sun bukaci jama’a da su yi taka-tsantsan da kuma sanar da hukuma idan sun ga wani ko wasu mutane masu dauke da raunin harsashi.

'Yan sanda na farautar sauran 'yan bindigar

Kwamishinan 'yan sandan Katsina ya aika sako ga mazauna jihar bayan dakile harin 'yan bindiga
'Yan sanda sun nemi mazauna Katsina su kai rahoton wadanda aka gani da raunin bindiga. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa ya yabawa jami’an tsaro kan yadda suka yi gaggawar dakile harin.

Ya kuma tabbatar da cewa an fara bincike domin gano inda ragowar ‘yan bindigar suka fake, yayin da ya ce kokarin kamo sauran ‘yan bindigar yana gudana tare da hadin gwiwar dakarun tsaro.

Kara karanta wannan

Wani abin fashewa ya tarwatse da jami'an 'yan sandan Najeriya a jihar Borno

A karshe, ya bukaci al’ummar jihar Katsina da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai domin kare lafiyarsu, rayukansu da dukiyoyinsu.

'Yan sanda sun dakile harin garkuwa da mutane

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an ƴan sandan Katsina sun ceto aƙalla mutum 18 da ƴan bindiga suka sace, bayan dakile harin da aka kai a hanyar Funtua-Gusau, Zamfara.

Rundunar ƴan sandan ta kuma yi nasarar ƙwato shanu masu yawa bayan daƙile yunƙurin satarsu a ƙauyen Gidan Gada da ke ƙaramar hukumar Kafur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.