Sanusi vs Aminu Ado: An Gargadi Abba da Sauran Hukumomi bayan Hukuncin Kotu
- Alhaji Aminu Babba Dan’agundi ya bukaci gwamnati da hukumomi su girmama umarnin kotun daukaka kara dangane da rikicin sarautar Kano
- Dan’agundi ya jaddada cewa doka ta bukaci a dawo da al’amura yadda suke kafin shari’ar ta fara a kotu kan rigimar da aka dade ana yi a Kano
- Ya bukaci wadanda aka nada bisa dokar 2024 su ajiye mukamansu domin girmama umarnin kotun daukaka kara har zuwa lokacin hukuncin Kotun Koli
- Kotun daukaka kara ta hana gwamnati da majalisa aiwatar da hukunci har sai kotun koli ta yanke hukunci na karshe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Yayin da ake ci gaba da rigima kan sarautar Kano, Alhaji Aminu Babba Dan’agundi ya ba hukumomi shawara.
Dan'agundi na daya daga cikin wadanda suka tsaya a rikicin sarautar Kano, ya bukaci a bi umarnin kotu da cikakken ladabi.

Kara karanta wannan
Sanusi II vs Aminu Ado: Halin da ake ciki a Kano bayan umarnin kotu kan masarauta

Asali: Twitter
Kotu ta ba da umarni kan rigimar sarautar Kano
Aminu Danagundi ya yi wannan magana ne a ranar Asabar, yayin da yake ganawa da 'yan jarida a fadar Nasarawa, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun daukaka kara ta bayar da umarni cewa a bar komai yadda yake kafin kotun koli ta yanke hukunci kan wannan rikicin sarauta.
Rahotanni sun ruwaito cewa kotun daukaka kara ta hana aiwatar da hukuncin da aka yanke har sai an saurari karar a kotun koli.
Jerin wadanda ake kara kan rigimar sarauta
Wadanda ake kira da sunayensu a cikin karar sun hada da majalisar dokokin jihar Kano da kuma wasu hukumomin gwamnati na jihar da jami'an tsaro.
Kotun ta kuma umurci wanda ya shigar da karar da ya rubuta takardar alkawari cikin sa’o’i 48 don biyan diyya idan bukatar ta fadi.

Asali: Facebook
Rigimar sarauta: Gargadin Dan'agundi ga gwamnatin Kano
Babba Dan'agundi ya jaddada cewa duka bangarorin da ke da hannu, ciki har da jami’an tsaro, dole su mutunta umarnin kotu don tabbatar da zaman lafiya a Kano.
Dan'agundi ya kuma shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya girmama wannan umarni da kotun ta bayar a ranar Juma’a.
A cikin jawabinsa, Dan'agundi ya ce:
“A bayyane umarnin kotu yake, a dawo da yadda abubuwa suke kafin a kai karar zuwa kotu."
Dan'agundi ya kuma bayyana cewa wadanda aka nada bisa dokar da aka soke, dole su bar kujerunsu don su mutunta wannan hukunci na kotu.
Gwamnatin Kano ta magantu kan rigimar sarauta
A baya, kun ji cewa Gwamnatin Kano ta ce hukuncin kotun daukaka kara bai soke dawo da Muhammadu Sanusi II matsayin Sarkin Kano ba.
Kwamishinan shari'a, Haruna Isa Dederi ya ce hukuncin ranar 10 ga Janairu ya tabbatar da ikon gwamnati na dawo da Sanusi kan karaga.
Kotun ta ce a ci gaba da zama a matsayin da ake ciki yanzu har sai kotun koli ta yanke hukunci kan karar da ake ci gaba da yi wanda ya ki ci ya ki cinyewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng