Sanusi II vs Aminu Ado: Halin da Ake ciki a Kano bayan Umarnin Kotu kan Masarauta
- Al'ummar jihar Kano na ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da matsala ba bayan umarnin kotu
- A jiya Juma'a ne Alkalin Kotun Daukaka Kara a Abuja ya dakatar da aiwatar da hukuncin da ya tabbatar da dawowar Sanusi II
- Alkalai uku sun amince da dakatar da hukuncin baya har sai kotun koli ta yanke hukunci kan karar da ke gabanta yanzu
- Gwamnatin Kano ta shirya taron manema labarai kan hukuncin, amma ta dage taron bayan ‘yan jarida sun hallara a gidan gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Ana ci gaba da gudanar da lamura a Kano lami lafiya bayan umarnin kotun daukaka kara kan rigimar sarauta.
Kotun daukaka kara dake Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin ranar 10 ga Janairu da ya tabbatar da dawowar Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarki.

Asali: Twitter
Sarautar Kano: Wane umarni kotu ta bayar?
Leadership ta ce wannan hukunci ya tabbatar da soke dokar da ta kafa masarautu a 2019 da gwamnatin Kano ta yi, har sai kotun koli ta yanke hukunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke umarnin da kotun tarayya da ke Kano ta bayar ranar 20 ga Yuni, 2024.
Kotun ta ce alkalin kotun tarayya, Abubakar Liman, bai da hurumin bayar da irin wannan hukunci kan batun masarautar Kano.
Kotun ta amince da wannan bukata a zaman da alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari'a Okon Abang suka gudanar a Abuja.
An bayyana cewa karar Aminu Babba Danagundi ce ta haddasa wannan mataki, inda ya kalubalanci gwamnatin Kano da wasu hukumomi.

Asali: Twitter
Hukuncin kotu a ranar 10 ga watan Janairu
Alkali Gabriel Kolawole ya yanke hukuncin cewa soke nadin Sanusi II an yi shi ba tare da hurumi ba, ya umarci a mayar da karar Kano.
Kotun daukaka kara ta ce bukatar dakatar da aiwatar da hukuncin baya tana da amfani kuma ya dace da doka da adalci.
Alkali Abang ya ce batun ya na bukatar kulawa saboda Sanusi II ya taba zama Sarki har na tsawon shekaru biyar kafin a sauke shi.
A hukuncin da aka yanke ranar 10 ga Janairu, Justice Kolawole ya ce batun shugabanci masarauta ya kamata ya tsaya a kotun jihar Kano.
Kotun tarayya da ke Kano karkashin Liman ta soke dokar da ta dawo da Sanusi II matsayin sarkin Kano ranar 20 ga Yuni.
Al'ummar na gudanar da lumuransu lami lafiya
Gwamnatin Kano ta yi niyyar gudanar da taron manema labarai game da hukuncin, amma an dage bayan ‘yan jarida sun isa gidan gwamnati.
Mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir, Sunusi Bature, ya bayyana cewa za a sanar da sabon lokaci da rana domin gudanar da taron.
Rahotanni sun ruwaito cewa jama’a sun ci gaba da ayyukansu kamar yadda aka saba, suna halartar tafsiri da shirin buda baki cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan
Aminu vs Sanusi II: An bayyana sahihin sarkin Kano bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara
Gwamnatin Kano ta magantu bayan hukuncin kotu
Kun ji cewa Gwamnatin Kano ta yi magana kan hukuncin kotu inda ta ce umarnin bai soke dawo da Muhammadu Sanusi II matsayin Sarki ba.
Kwamishinan shari'a, Haruna Isa Dederi ya ce hukuncin ranar 10 ga Janairu ya tabbatar da ikon gwamnati na dawo da Sanusi kan karaga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng