'Yan Bindiga Sun Kashe Mahaddacin Kur'anin da Suka Sace a Katsina? An Gano Gaskiya

'Yan Bindiga Sun Kashe Mahaddacin Kur'anin da Suka Sace a Katsina? An Gano Gaskiya

  • Gwamnatin jihar Katsina ta taɓo batun da ke yawo na cewa ƴan bindiga sun kashe mahaddacin Al-Ƙur'anin da suka sace a Faskari
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya tabbatar da cewa har yanzu matashin, mahaifinsa da ɗan uwansa suna hannun ƴan bindiga
  • Dr. Bala Salisu-Zango ya kuma bayyana cewa ƴan bindiga sun buƙaci N30m a matsayin kuɗin fansa kafin su sako mutanen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta yi magana kan halin da matashin da ya haddace Al-Kur'ani wanda ƴan bindiga suka sace yake ciki.

Gwamnatin ta bayyana cewa Abdulsalam Rabiu Faskar, mahaifinsa da ɗan uwansa har yanzu suna raye amma suna hannun masu garkuwa da su.

'Yan bindiga sun sace mahaddacin Kur'ani a Katsina
Gwamnatin Katsina ta tabbatar da sace mahaddacin Al-Kur'ani Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da dl’adu, Dr Bala Salisu-Zango, ya fitar a ranar Juma’a a Katsina, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza fada da 'yan bindiga, sun hallaka miyagu a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba dai ƴan bindiga sun sace su ne a hanyarsu ta komawa Faskari daga Katsina, bayan da Gwamna Dikko Radda ya karrama su.

Gwamna Radda ya karrama su ne saboda bajintar da Abdulsalam Rabiu Faskari ya nuna a gasar karatun Al-Ƙur’ani ta ƙasa da aka gudanar a Kebbi.

Me gwamnati ta ce kan sace mahaddacin Al-Ƙur'ani

Kwamishinan ya bayyana cewa matashin zai wakilci Najeriya a gasar karatun Al-Ƙur’ani ta duniya da za a gudanar nan gaba.

"Gwamnatin jihar Katsina ta samu labarin rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai da kuma saƙon ta’aziyya da ke cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan Kebbi kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kai ya fitar."
“Sanarwar ta yi iƙirarin cewa an kashe Abdussalam Rabiu Faskari, wanda ya lashe gasar karatun Al-Ƙur’ani ta ƙasa, kuma dalibi a ajin karshe na fannin likitanci a jami’ar ABU."

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige gwamna ya jefa Shugaba Tinubu a matsala, an yi masa barazana

"Muna godiya ga gwamnatin jihar Kebbi bisa kulawa da tausayi da ta nuna kan wannan lamari mara daɗi."
"Duk da haka, muna so mu fayyace cewa haƙiƙa ƴan bindiga sun sace Abdulsalam Rabiu Faskari, mahaifinsa da ɗan uwansa."
“Amma bayanai da suka isa ga gwamnati sun nuna cewa har yanzu suna raye kuma lafiyarsu kalau a hannun masu garkuwa da su."

- Bala Salisu-Zango

Kwamishinan ya ƙara da cewa ya zuwa ranar Juma’a, masu garkuwar suna buƙatar kudin fansa na Naira miliyan 30 daga iyalansu.

Gwamnan jihar Katsina ya nuna takaicinsa

Kwamishinan ya naƙalto Gwamna Dikko Umaru Radda yana bayyana sace ɗalibin tare da mahaifinsa da ɗan uwansa a matsayin abin takaici.

Gwamnan ya buƙaci jami’an tsaro su haɗa kai domin ganin an ceto su cikin ƙoshin lafiya.

Dikko Radda ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na shawo kan matsalar tsaro da ke addabar jihar.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun yi rashin imani, sun tashi mutanen garuruwa 5 ana azumi

Haka kuma, ya buƙaci al’umma da su yi addu’a domin kuɓutar Abdulsalam Rabiu Faskari da duk sauran waɗanda ke hannun miyagu.

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun ƴan bindiga sun kai hare-hare a wasu ƙauyuka uku na ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Miyagun ƴan bindigan a yayin hare-haren na ta'addanci da suka kai a tsakiyar dare, sun yi awon gaba da mutum 10 zuwa cikin daji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel