Ana Daf da Cafke Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ake Nema Ruwa a Jallo bayan Kama Hadiminsa

Ana Daf da Cafke Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ake Nema Ruwa a Jallo bayan Kama Hadiminsa

  • Rundunar tsaro sun ƙara ƙaimi wajen farautar shugaban ƴan bindiga, Kachalla Dan Mai Kinni, bayan cafke abokinsa Lawali Malangaro
  • Bayanai sun nuna cewa Malangaro, ɗan asalin Tsibiri, an kama shi ne a Galadi ta hannun 'yan sa-kai da ke yaki da ƴan bindiga a Zamfara
  • Malangaro yana da alaƙa da satar shanu da kudi, yana kula da harkokin Kachalla Dan Mai Kinni a Kaura Namoda da Shinkafi da Zurmi
  • Dan Mai Kinni yana jagorantar gungun ƴan bindiga masu makamai, suna addabar al'ummomin Galadi, Tsibiri da Tubali da hare-haren tashin hankali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - A kokarin kakkabe ƴan bindiga musamman a Arewacin Najeriya, sojoji suna samun nasara kan gungun yan bindiga da ke addabar al'umma.

Dakarun tsaro sun ƙara ƙaimi wajen neman Kachalla Dan Mai Kinni, fitaccen shugaban ƴan bindiga, bayan kama abokin tafiyarsa Lawali Malangaro a Tsibiri a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza fada da 'yan bindiga, sun hallaka miyagu a Zamfara

Sojoji sun cafke hadimin rikakken dan bindiga a Zamfara
Rundunar sojoji sun kama na hannun daman hatsabibin ɗan bindiga. Hoto: Legit.
Asali: Original

An hallaka dan bindiga, Kachallah Dogo a Zamfara

Majiyoyin leƙen asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa an cafke Malangaro, wanda ɗan asalin Tsibiri ne, a garin Galadi ta hannun ‘yan sa-kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Sojojin 'Operation Fansan Yanma' sun kashe 'yan ta'adda 12 a kauyen Maigora da ke ƙaramar hukumar Faskari, inda suka kwato babura da dama daga hannunsu.

Daga cikin wadanda aka kashe akwai wani shahararren shugaban 'yan bindiga mai suna Kachallah Dogo, wanda aka tabbatar da mutuwarsa.

Rahotanni sun ce Dogo wani shugaban gungun ‘yan bindiga ne da aka kashe a artabun da dakarun suka yi da su a yankin.

Hakan bai rasa nasaba da kokarin jami'an sojoji wurin tabbatar da kakkabe ayyukan ta'addanci a Arewa da sauran yankunan kasa wanda ya yi sanadin rasa rayukan al'umma da dama.

Yadda sojoji suka cafke hadimin rikakken dan bindiga a Zamfara '
Yayin da ake neman dan ta'adda ruwa a jallo, sojoji sun cafke hadiminsa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Yadda ɗan bindiga ya addabi al'ummar Zamfara

Ana zargin Malangaro da kasancewa jigo a cikin ƙungiyar Dan Mai Kinni, yana kula da shanun sata da kuɗaɗen ayyukan ta’addanci.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

An tabbatar cewa dan ta'addan ya fi kaurin suna a shiyyoyin Kaura Namoda da Shinkafi da Zurmi, har zuwa gabashin Sokoto.

Kachalla Dan Mai Kinni yana jagorantar gungun ‘yan bindiga masu ƙarfi da manyan makamai inda suke kai hare-hare kan al'umma.

Daga cikin yankunan da yake addaba akwai Galadi da Tsibiri da Tubali da hare-haren tashin hankali.

Ƴan bindiga sun sace ɗan Isiyaka Rabi'u

Mun ba ku labarin cewa wasu yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji sun sace wani mutum da ya bayyana kansa a bidiyo a matsayin ɗan Isiyaka Rabiu, yana roƙon a biya kudin fansa.

An yada bidiyon a kafafen sada zumunta wanda ya nuna matashin cikin damuwa, yana kira ga danginsa su cika sharuddan 'yan bindiga don kubutar da shi.

An ce majiyoyi sun tabbatar cewa dan bindiga, Turji ya buya bayan farmakin sojoji, inda shi da Dan Isuhu suka tsere, ba tare da bulla a kafafen sada zumunta ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel