Albarkacin Azumi: Yadda Almajirai Suka Yi Cudanya da Gwamnan Nasarawa

Albarkacin Azumi: Yadda Almajirai Suka Yi Cudanya da Gwamnan Nasarawa

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya raba sadaka ga almajirai da marasa galihu sama da 500 a garin Lafia
  • Mai girma Abdullahi Sule ya bayyana cewa ya yi hakan ne don neman lada da yardar Allah a watan Ramadana
  • Biyo bayan lamarin, mutane sun bayyana ra’ayoyinsu kan hakan, wasu na yabawa, wasu kuma na caccakar gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi A. Sule, ya raba sadaka ga almajirai da marasa galihu sama da 500 a ranar Juma’a.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa ya raba kudin ne a matsayin sadaka don neman lada a watan Ramadana da ake azumi a duniya.

Nasarawa
Almajirai sun yi cudanya da gwamnan Nasarawa wajen karbar sadaka. Hoto: Gov. Abdulahi Sule Mandate
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da gwamnan ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Wata mata ta rasu a wani irin yanayi yayin tafsirin Kur'ani a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin gwamnan ya samu karbuwa daga wasu mutane, yayin da wasu kuma suka soki lamarin, suna masu cewa kamata ya yi a samar da ingantaccen tsarin karatu ga yaran da ke gararamba.

Gwamna Sule ya bayyana dalilin yin sadaka

A lokacin rabon tallafin, Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa wannan kyauta sadaka ce ta kansa ba wai daga gwamnati ba.

Ya raba sadakar ne da fatan hakan zai taimaka wa marasa galihu musamman a cikin watan Ramadana, wata mai falala ga Musulmi.

Gwamnan ya ce:

"Na yi haka ne don neman yardar Allah, ba wani dalili ba,"

Martanin jama’a kan sadakar gwamnan

Bayan da aka wallafa hotunan rabon sadakar a shafukan sada zumunta, mutane da dama sun yi martani kan lamarin, wasu na yabawa, wasu kuma na caccaka.

Wani mai suna Abdullahi Muslim ya ce:

"Ka burge ni sosai. Allah ya ƙara albarka kuma ya kare ka daga makiya."

Kara karanta wannan

'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu

Sai dai wani mai suna Onah Kingsley ya caccaki lamarin, yana mai cewa:

"Kashi 80% na wadannan yara ba sa zuwa makaranta amma gwamnati ba ta yin komai a kai. Ga abin da gwamna ke rabawa, kuma jami’ansa suna daukar hoto suna wallafawa."

Wata mai suna Habiba Ibrahim Odeh ta ce:

"Allah ya biya, Mai girma Gwamna."

Wani mai suna Rector Funs kuwa ya ce:

"Ana neman yardar Allah, amma ana daukar hotuna a kowane wuri."

Legit ta tattauna da malamin addini

Wani malamin addini a jihar Bauchi, Malam Abubakar Kari ya zantawa Legit cewa kowa na iya yin sadaka a matakinsa, ko da shugaba ne.

NAsarawa
Gwamna Abdullahi Sule na raba sadaka. Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Asali: Facebook

Malamin ya ce yin sadakar gwamna abu ne mai kyau duk da cewa zai fi samun lada idan ya sauke nauyin da ke kansa yadda ya kamata.

"Babu laifi gwamna ya yi sadaka. Watakila hakan ma ya zamo abin koyi ga wasu makusantansa.

Kara karanta wannan

Sheikh Guruntum ya ba da mamaki, ya ƙi karbar kyautar miliyoyi daga wani Alhaji

"Idan ya yi da zuciya daya, lallai zai samu lada."

- Malam Abubakar Kari

Sheikh Guruntum ya ki karbar kyauta

A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya ki karbar wasu makudan kudi.

Rahoton Legit ya nuna cewa wani Alhaji ne ya ba Sheikh Guruntum kyautar kudi kimanin Naira miliyan 10 a lokacin bikin 'ya'yansa amma ya ki karba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel