SDP Ta Tono 'Makarkashiyar' da Gwamnatin APC Ke Shiryawa El Rufai

SDP Ta Tono 'Makarkashiyar' da Gwamnatin APC Ke Shiryawa El Rufai

  • Kwanaki kaɗan bayan komawar Nasir Ahmad El-Rufai zuwa SDP, jam'iyyar ta fara zargin ana shirin murƙushe ƴan adawa
  • SDP ta yi zargin cewa APC na son amfani da ikon gwamnati wajen hana ƴan adawa sauya sheƙa zuwa cikinta ta hanyar yi musu barazana
  • Jam'iyyar ta yi zargin cewa gwamnati ta shirya ƙirƙiro tuhume-tuhume na ƙarya kan tsohon gwamnan jihar Kaduna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar SDP mai adawa ta yi sabon zargi kan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Jam'iyyar SDP ta zargi APC da yin amfani da jami’an tsaro wajen razana ƴan adawa.

SPD ta yi zargi APC kan El-Rufai
SDP ta yi zargin ana shirin tuhumar Nasir El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin SDP, Rufus Aiyenigba, ya fitar a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SDP ta fallasa shirin jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Tsofaffin ministocin Buhari 10 da manyan ƙusoshi na shirin bin El Rufai zuwa SDP

Rufus Aiyenigba ya bayyana cewa wannan matakin na amfani da jami'an tsaron, na da nufin hana shugabannin ƴan adawa sauya sheƙa zuwa SDP.

"Muna da labarin cewa ana shirin danne fitattun ƴan adawa domin haddasa tsoro a cikin harkokin siyasa."
"Wannan dabara an shirya ta ne domin hana sauya sheƙa zuwa jam’iyyarmu ta hanyar amfani da dabarun tsoratarwa."
“SDP ta samu sahihan bayanai da ke nuna cewa APC ta damu kan yadda jam’iyyarmu ke ƙara samun ƙarfi."
"Don haka, APC ta yanke shawarar amfani da ikon gwamnati wajen ƙirƙiro tuhume-tuhumen ƙarƴa kan mambobinmu."

- Rufus Aiyenigba

Wace maƙarƙashiya ake shiryawa El-Rufai?

Rufus Aiyenigba ya yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda kwanan nan ya koma SDP, shi ne babban wanda jam’iyya mai mulki ke shirin fara tuhuma, rahoton Tribune ya tabbatar.

"Gwamnati na shirin gurfanar da shi da tuhuma da dama a Abuja da Kaduna nan ba da jimawa ba."

Kara karanta wannan

"Ba mu yarda ba," El Rufai ya ƙara shiga matsala bayan komawa SDP, matasa sun masa rubdugu

"Domin cimma wannan buri, mun kuma samu labarin cewa gwamnatin tarayya ta ba da umarni ga hukumominta da su hana Malam Nasir El-Rufai barin ƙasar nan."

- Rufus Aiyenigba

Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin jihar Kaduna ma tana bin sawun gwamnatin tarayya wajen yin barazana ga ƴan adawa.

"A Kaduna ma, gwamnatin jihar na bin sawun gwamnatin tarayya wajen yi wa shugabannin adawa barazana."

- Rufus Aiyenigba

Rufus Aiyenigba ya bayyana ƙoƙarin murƙushe 'yan SDP a matsayin sabon salo na danniya da kuma barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.

Ministan Tinubu ya ragargaji Nasir El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Yusuf Ata, ya yi martani mai zafi ga Nasir El-Rufai kan sukar shugaba Bola Tinubu.

Ministan ya bayyana tsohon gwamnan na jihar Kaduna a matsayin wanda har yanzu yake jin zafi sakamakon rasa samun gurbi a gwamnatin Tinubu.

Ya zargi El-Rufai da gazawa a lokacin da yake gwamna wajen samar da tsaro da kare rayukan al'ummar jihar Kaduna, musamman na yankin Kudancinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel