Kano: Ganduje, Gwamnatin Abba Sun Jingine Bambancin Siyasa don Taimakon Talakawa
- Darakta a REA, Injiniya Umar Abdullahi Ganduje, ya ce hukumarsa za ta hada kai da gwamnatin Kano domin samar da wutar lantarki mai dorewa
- Ya dauki alkawarin ne a lokacin da tawagar gwamnatin Kano, a karkashin jagorancin kwamishinan wutar lantarki, Gaddafi Sani Shehu ta ziyarce shi
- Gwamnatin jihar Kano da REA sun tattauna hanyoyin faɗaɗa ayyukan makamashi mai tsafta a bangarori kamar kiwon lafiya, ilimi, noma, da sufuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano ‐ Babban darakta na hukumar wutar lantarkin karkara (REA), Injiniya Abba Ganduje, ya jaddada kudirin hukumar na tallafa wa shirin Kano na bunkasa makamashin zamani.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi wata babbar tawaga daga gwamnatin jihar Kano a Abuja kan yadda za a wadata talakawan Kano da hasken wutar lantarki mai dore wa.

Asali: Facebook
A shafinsa na Facebook, kwamishinan wutar lantarki da makamashi mai dorewa, Dr. Gaddafi Sani Shehu, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce an tattauna yadda za a samar da wutar lantarki fadin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattauna dabarun faɗaɗa ayyukan makamashi mai dorewa don inganta wutar lantarki a bangarorin kiwon lafiya, ilimi, noma, al’ummomin karkara da harkokin sufuri.
Ganduje ya tarbi tawagar gwamnatin Kano
A karin bayani da ya yi ga Legit ta manhajar WhatsApp, babban darakta na yada labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Injiniya Abba Ganduje ya tarbi tawagar gwamnatin Kano.
Ya jaddada cewa hukumar REA za ta ci gaba da haɗin gwiwa da jihar Kano domin tabbatar da hanyoyin samar da wutar lantarki mai dorewa.

Asali: Facebook
Injiniya Ganduje ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen inganta rayuwar jama’a tare da bunkasa tattalin arziki.
Ya ce:
"Mun kuduri aniyar aiki kafada da kafada da jihar Kano domin aiwatar da manyan ayyukan makamashi mai dorewa da za su inganta muhimman sassa kuma su sauya rayuwar mazauna jihar."
Abin da ya kai gwamnatin Kano ga Ganduje
A yayin taron, bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin inganta haɗin gwiwa a nan gaba, inda suka jaddada muhimmancin makamashi mai tsafta wajen samar da ci gaba.
Haka kuma an gana kan muhimmancin samar da wutar lantarki mai dorewa ga hukumomin gwamnati da al’ummomin karkara a Kano.
Taron ya zama wani muhimmin mataki a kokarin jihar Kano na sauya fasalin samar da makamashi, inda hukumar REA ta tabbatar da bayar da tallafi na fasaha da dabaru
Tawagar gwamnatin Kano da ta ziyarci Ganduje
Tawagar Kano da ta ziyarci Ganduje ta kunshi kwamishinonin ilimi, sufuri, da ci gaban karkara da al’umma, tare da shugabannin hukumar wutar lantarki ta karkara (REB) da kuma KanInvest.
Haka kuma, mai ba gwamna shawara na musamman kan lafiya kuma likitansa, Dr. Ibrahim Musa, ya kasance a wurin, tare da jagorancin kwamishinan wutar lantarki da makamashi mai dorewa, Injiniya Dr. Gaddafi Sani Shehu.
Ganduje: "Za mu kwace wasu jihohi daga PDP"
A baya, kun samu labarin cewa shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce jam’iyyarsa na da shiri na musamman domin kwato jihohin Oyo da Osun daga hannun PDP a zaɓen 2027.
Ganduje, wanda ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya karɓi Dr. Gbenga Adegbola, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a hukumance ya ce APC na kara karfi matuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng