Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Yi Rashin Imani, Sun Tashi Mutanen Garuruwa 5 ana Azumi
- Ƴan bindiga sun kai farmaki kauyuka biyar da ke yankin karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna, sun kori mutane daga gidajensu
- Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun ƙona kayayyakin mutane, sun kuma yi garkuwa da wasu matasa a kudancin jihar
- Shugaban al'umma a yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ƴan bindigar sun shiga kauyukan ɗauke mugayen makamai, suka buɗe wuta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Wasu ƴan bindiga da suka gudo daga luguden sojoji sun tarwatsa mutanen garuruwa biyar a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta'addan sun tilasta wa mutane guduwa daga gidajensu a Unguwan Tauka, Unguwan Lalle, Sonudazuwa, Tsauni Dodo, da Dandauka.

Asali: Original
Wani jagoran al’umma a yankin ya shaida wa Daily Trust cewa maharan sun kuma afkawa wani sansanin Fulani a Kubuwo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindiga sun tarwatsa garuruwa 5
Ya ce ƴan ta'addan sun sace wasu makiyaya matasa guda uku, sanann sun ƙona motoci da shagunan mutane a kauyuka biyar da aka bayyana a sama.
A cewarsa, lamarin ya faru ne ranar Alhamis da ta gabata da misalin karfe 6:00 na yamma, lokacin da ‘yan bindigar dauke da makamai suka kutsa kai cikin garuruwan.
Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun buɗewa mazauna garuruwan wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya tilasta masu guduwa, rahoton Punch.
Sojoji sun fatattako ƴan bindiga daga jeji
Wani daga cikin mutanen da abin ya shafa ya ce maharan sun shigo yankin ne a kokarin tserewa luguden sojoji a dajin Kurutu-Azara, wanda ke iyaka da ƙaramar hukumar Kagarko.
A cewarsa, dakarun sojoji ne suka matsawa ƴan ta'addan, suka gudo zuwa wasu kauyuka, inda suka ci zarafin jama’a tare da kwashe dukiyoyinsu.
Wani ganau ya ce:
"‘Yan bindigar sun gudo ne daga farmakin sojoji a dajin Kurutu, amma maimakon su tsere, sai suka rika farmakar kauyuka, suna harbi tare da sace mutane da dabbobi."
Mahara sun tafka ta'adi a jihar Kaduna
A Unguwan Tauka, maharan sun banka wa wata mota da babur wuta bayan da suka kasa yin garkuwa da wasu mazauna kauyen.
"Mutumin da aka ƙona motaraa ya dawo ne daga Kaduna bayan ya sayo sabuwar mota, da ya ga ƴan bindigar sai ya sauka ya gudu, su kuma suka ƙona motar," in ji ganau.

Asali: Getty Images
‘Yan sandan da ke aiki a yankin sun tabbatar da harin amma kuma sun bukaci a tuntuɓi hedikwatar rundunar da ke Kaduna don karin bayani.
Har zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Kaduna, ASP Hassan Mansur, ba kan waɗannan sababbin hare-hare masu muni.
Sojoji sun rage mugun iri a Kaduna
A baya, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi artabu da ƴan bindiga a kan babban titin nan na Kaduna zuwa Abuja.
Dakarun sojin Operation Fansan Yamma sun kashe uku daga cikin 'yan ta'addan a harin kwanton bauna da suka kai masu a kusa da tsaunin Ngwagi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng