Bayan Shafe Shekaru Ana Rigimar Limanci, Kotu Ta Shiga Lamarin a Azumin Ramadan

Bayan Shafe Shekaru Ana Rigimar Limanci, Kotu Ta Shiga Lamarin a Azumin Ramadan

  • Kotu da ke yankin Iragbiji a jihar Osun ta ci gaba da sauraron karar da ke tsakanin wadanda ke takarar matsayin babban limamin Inisha
  • Rikicin ya samo asali ne bayan nada Abdulazeez Tijani a matsayin limami, yayin da wasu suka fi son Alhaji Abdulakeem Muhammadu Jamiu
  • Gwamna Ademola Adeleke da kungiyar limamai sun shiga tsakani bayan garin Inisha ya shafe shekaru babu limami saboda sabanin ra’ayi
  • Wani shaida ya bayyana cewa an nada limaman biyu a rana guda a masallaci daya, lamarin da ya haddasa rikici na kwana da kwanaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Babbar kotun jihar Osun da ke Iragbiji, hedkwatar karamar hukumar Boripe, ta ci gaba da sauraron shari'ar nada limamin Inisha a Odo-Otin.

Shari’ar na gudana tun daga shekarar 2021, bayan rikicin da ya biyo bayan nadin sabon limami wanda ya janyo rashin zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Yaki da zaman banza: Tinubu na shirin samar da ayyuka ga matasa miliyan 10

Kotu ta shiga lamarin rigima da ake yi kan limancin masallaci
Gwamna Ademola Adeleke ya tsoma baki kan rigimar limanci a Osun. Hoto: Legit.
Asali: Original

Rigimar shugabanci ya rikice a masallaci

Bayan nadin limamin, wasu Musulmai a garin sun nuna goyon baya ga Abdulazeez Tijani, yayin da wasu suka fi son Abdulakeem Muhammadu Jamiu, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya, mun ruwaito muku cewa rigima ta barke kan shugabanci a Masallacin Darul Hadith da ke Tudun Yola a Kano da ya kawo cikas yayin Sallar Jumu'a ranar 6 ga watan Janairun 2025.

Rahotanni sun tabbatar cewa bayan matsalar da aka samu, jami'an yan sanda sun ba da tsaro har aka gama Sallah a masallacin .

Kakakin yan sanda a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tuni aka gayyaci bangarorin biyu domin lalubo bakin zaren da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Gwamna ya shiga tsakani kan rigimar limancin masallaci
Rigimar masallaci a Osun ta yi kamari bayan kai lamarin gaban kotu. Hoto: Gov. Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

Rigimar limanci ya munana har zuwa kotu

Saboda rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu, garin ya shafe shekaru ba tare da limami ba har sai da gwamnati ta shiga tsakani.

Gwamna Ademola Adeleke tare da kungiyar limamai sun shiga tsakani domin warware rikicin da ya jima yana addabar garin.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta girgiza Tinubu: Babban farfesan jami'ar ABU ya rigamu gidan gaskiya

Yayin sauraron shari’ar, lauyan mai karar, Jimoh Abdulmumini, ya sanar da kotu cewa limamai biyu aka nada a rana guda, cewar The Sun.

Musabbabin rigimar da ta balle a masallaci

Jimoh ya bayyana wa kotu cewa wannan abin ya jawo rikici mai tsanani a cikin garin Inisha da ke yankin Odo-Otin.

Wani mai ba da Shaida, Jimoh Ibrahim, ya ce an nada limami na farko da safe, sannan na biyu da yamma, a masallaci guda, wanda ya haddasa fitina.

Mai shari’a G.O. Lawal ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Mayu, 2025 domin cigaba da shari’a.

Gwamnati ta hana sallah a masallaci a Lagos

Kun ji cewa rigima ta kaure kan limanci a wani masallaci da ke yankin ƙaramar hukumar Agege a jihar Lagos bayan rasuwar babban liman.

Shugaban ƙaramar hukumar Agege, Ganiyu Egunjobi ya ba da umarnin rufe masallacin nan take domin gudun tashin-tashina a yankin.

Kara karanta wannan

Malaman addini sun haɗa kai, sun tunkari Bola Tinubu kan tsadar rayuwa

'Dan siyasar ya ce za a shirya zama da dukkan ɓangarorin biyu domin lalubo mafita da kuma magance yiwuwar tada zaune tsaye ƙafin sake buɗe masallacin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel