Majalisa za Ta Zauna kan Kudirin Harajin Tinubu kafin Amincewa da Shi

Majalisa za Ta Zauna kan Kudirin Harajin Tinubu kafin Amincewa da Shi

  • Majalisar wakilai za ta yi nazari daga sashe zuwa sashe kan rahotannin kudirin gyaran haraji da kwamitin sauraron ra’ayoyin jama’a ya tattaro
  • Shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, ya bukaci dukkan ‘yan majalisar su kasance a wurin domin tabbatar da cewa an duba ra'ayoyin yadda ya dace
  • Daga cikin kudirin dokar da aka gabatar akwai soke dokar kafa hukumar tattara haraji ta kasa, sannan a kirkiri wata sabuwa da ikon majalisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMajalisar wakilai za ta fara duba rahotannin kudirin gyaran haraji da kwamitin sauraron ra'ayoyin jama'a ya tattaro mata a ranar Alhamis.

Shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, wanda ya sanar da hakan kafin a dage zaman majalisar a ranar Laraba, ya bayyana cewa za a ware zaman ranar Alhamis don duba kudurorin.

Kara karanta wannan

"Babu wanda zai dawwama a mulki," Gwamna ya ji haushin abin da aka masa a Majalisa

majalisa
Za a fara tsefe kudirin haraji bayan sauraron ra'ayoyin jama'a Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya kuma bukaci ‘yan majalisar da su tabbata sun halarci zaman domin su taka rawa a tantance rahoton da kuma karɓarsa a hukumance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Talatar da ta gabata ne, shugaban kwamitin majalisar kan kudi, James Abiodun Faleke, ya gabatar da rahotannin da suka shafi hadakar kudurin gyaran haraji bayan sun dawo daga hutu.

Majalisa ta karɓi rahoton kwamitin kudirin haraji

BBC Hausa ta wallafa cewa miƙa rahoton ga majalisa ya biyo bayan kammala zaman jin ra’ayoyin jama’a na kwanaki uku kan kudurin da kuma nazarin bayanan da aka gabatar.

Haka kuma, kwamitin ya shigar da shawarwari daga bangarori daban-daban na jama’a da suka ba da gudunmawa a zaman sauraron ra’ayoyin.

Majalisa
Shugaban majalisa ya umarci kowane dan majalisa ya halarci zaman duba kudirorin haraji Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Twitter

Daga cikin rahotannin da aka gabatar wa majalisa har da na kudirin doka da ke tanadar da tsarin tantancewa, karɓa da kuma lissafa kudaden shiga da ke shiga asusun tarayya, jihohi da kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

"Jonathan ya yi bankwana da siyasa," PDP ta magantu kan fito da shi takara

Majalisa: An gabatar neman gyaran kudirin haraji

Sauran kudirin dokokin da aka gabatar sun haɗa da kudirin doka na soke dokar kafa hukumar tattara haraji ta gwamnatin tarayya (FIRS) ta shekarar 2007.

Kazalika, an gabatar da kudirin doka na kafa hukumar haraji ta ƙasa, wacce ke da alhakin tantancewa, tara wa da kuma lissafa kudaden shiga da za su shiga asusun gwamnatin tarayya da sauran batutuwa masu nasaba da hakan.

Kakakin majalisar ya kuma bayyana cewa daga cikin kudurorin akwai:

"Kudirin kafa hukumar tattara haraji ta haɗin gwiwa, kotun ɗaukaka kara kan batun haraji da kuma ofishin mai sa ido kan haraji, domin daidaita, tsara da kuma warware sabani da ke tasowa daga harkokin gudanar da haraji a Najeriya."
"Kudirin soke wasu dokokin haraji da haɗa su a cikin doka guda domin kafa dokar haraji ta Najeriya, wadda za ta samar da tsarin haraji na kudaden shiga, mu’amaloli da takardu da sauran batutuwa masu nasaba da hakan."

Kara karanta wannan

Akpabio ya kalubalanci hurumin kotu kan koken Sanata Natasha

'Dan majalisa ya koka da kudirin haraji

A baya, mun kawo labarin cewa dan majalisar Katsina, Sada Soli, ya bayyana cewa an ba shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara mara kyau kan kudirin dokokin sauya fasalin haraji.

Ya yi wannan furuci ne yayin da majalisar wakilai ke ci gaba da mayar da maganganu a kan dokokin haraji guda huɗu da shugaban kasa ya mika gabatansu tun a shekarar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel