Kura Kurai 6 da Musulmi Ke Yi a Watan Azumi Ramadan da Yadda Za a Guje Masu

Kura Kurai 6 da Musulmi Ke Yi a Watan Azumi Ramadan da Yadda Za a Guje Masu

Ramadan wata ne mai alfarma da tarin albarka, rahama da gafara, wanda a cikinsa musulmi ke yin azumi, ibada, da duk wasu kyawawan ayyuka don neman yardar Allah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wannan wata ne da Musulmi ke ƙoƙarin ƙarfafa imaninsu, dagewa da ayyukan ibada, da kuma gyara halayensu ba don komai ba sai don neman kara kusanci da Allah SWT.

Watan azumi
Kura-kuran da mutane ke yi da hanyar kauce masu a Ramadan Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Duk da haka, mutane da dama suna yin wasu kura-kurai da ke rage ladan da za su samu, wasu kuma suna da illa ga lafiya.

A wannan babi, Legit Hausa ta tattaro maku cikakken bayani kan wasu kura-kurai da mutane ke yawan aikatawa a watan Ramadan da yadda za a guje musu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Barin Sahur

Ɗaya daga cikin kura-kurai da musulmai ke yi wasu ma sun ɗauke shi ba a bakin komai ba shi ne barin sahur, watau abincin da ake ci da asubah.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu

Mutane da dama kan ƙyale sahur su yi ɗore bisa dalilin barci ko kuma suna ganin cewa za su iya jure yin azumi koda ba su tashi sun ci abinci ba.

Abincin Sahoor.
Sahur ya na da matuƙar muhimnanci da falala a watan Ramadan Hoto: Geety Images
Asali: Getty Images

Wasu kuma su na barin Sahur saboda barci ko tunanin za su iya jurewa ba tare da cin abinci ba. Wasu kuma suna tashin Sahur amma suna cin abu kaɗan kamar ruwa ko shayi kawai.

Sahur yana da matukar muhimmanci da falala, Annabi (SAW) ya ce: "Ku tashi ku yi Sahur, domin a cikinsa akwai albarka." (Sahih Bukhari).

Saboda haka, yana da kyau a tashi a ci abinci mai gina jiki kamar hatsi, madara, ƙwai, da ‘ya’yan itatuwa domin samun kuzari na yini gaba ɗaya.

2. Cin abinci mai yawa da buda-baki

Wasu mutane su kan cika cikinsu da abinci mai nauyi da yawa bayan sun sha ruwa watau da magrib, wanda hakan ke sa su jin nauyi da kasala.

Kara karanta wannan

Kamfanin MAGGI zai fara shiri na musamman a watan Ramadan

Duk da mutane na kai azumin cikin matsananciyar yunwa da kishir ruwa amma cika abinci jim kaɗan bayan an sha ruwa ya na haifar da wasu matsaloli.

Abin da aka fi kwadaitarwa shi ne mutum ya bi sunnah ta Annabi (SAW) ta hanyar fara bude baki da dabino da ruwa ko ƴaƴan itatuwa irinsu kankana, sannan a jira kaɗan kafin cin abinci mai nauyi.

A guji cin abinci mai yawan mai ko sukari don kada ya haifar da kasala wacce ka iya hana mai azumi yin wasu ibadojin da ambatar Allah mai girma da ɗaukaka.

Cin abinci da yawa yana da illa a lafiya

Wani malamin asibiti da ke aiki a PHC Dabai, Muhammad Bello ya shaida wa Legit Hausa cewa cin abinci mai nauyi da daddare yana da illa a lafiya.

Ya ce an fi son mutum ya ci abubuwa masu ruwa-ruwa musamnan ƴaƴan itatuwa, irinsu kankana da sauran makamantansu.

Kara karanta wannan

An yi zazzafan martani ga gwamnatin tarayya kan hutun azumi a makarantun Arewa

Muhammad ya ce:

"A tsarin kiwon lafiya ba a son mutum ya cika cikinsa, haka ba a son cin abu mai nauyi irinsu shinkafa da daddare, dalili kuwa shi ne a bar tsarin markade abinci ya huta.
"Idan hanyar markaɗe abinci a jiki bai samu hutu ba, shi ne da safe za ka tashi da kasala, kuma yawaita wannan ɗabi'a yana kawo saurin tsufa da ciwuka iirinsu basir.
"A shawarce da azumin nan, idan aka sha ruwa, mutum ya samu kayan marmari ya ci, bayan ɗan lokaci ka ci abinci mai nauyi ɗan daidai, da asuba ka tashi ka yi sahur"

3. Rashin shan ruwa isasshe

Wasu mutane su na mantawa da shan ruwa isasshe daga lokacin bude baki har zuwa Sahur, wanda hakan ke sa su jin ƙishirwa da gajiya yayin azumi.

Yana da kyau musulmi ya tabbatar ya sha akalla kofi takwas (8) na ruwa tsakanin Iftar da Sahur, rahoton APN News.

Kara karanta wannan

'Muna cikin tashin hankali': Daruruwan mata sun fita zanga zanga a jihar Benuwai

Ruwan leda.
Shan ruwa isasshe ya na taimaka wa lafiya Hoto: Abdulhadi Ibrahim
Asali: Facebook

A guji shan shayi da shan giya saboda suna hana jiki riƙe ruwa. ‘Ya’yan itatuwa kamar kankana da kokwamba suna taimakawa wajen hana ƙishirwa.

Dangane da batun shan ruwa kuwa, Muhammad ya yi wa wakilin Legit bayanin cewa ruwa yana da matuƙar muhimmanci a lafiyar ɗan adam.

Ya ce a watan azumi, ana son mai azumi ya sha akalla kofi takwas zuwa 10 na ruwa, kwatankwacin lita buyu zuwa uku tsakanin buɗa baki da sahur.

"Ana buƙatar shan kofuna 8–10 na ruwa (kimanin lita 2–2.5) tsakanin Iftar (bude baki) da Sahur domin guje wa rashin ruwa a jiki, gajiya, da ciwon kai," in ji shi.

4. Ɓata Lokaci a soshiyal midiya

Bugu da ƙari, musulmi musamman matasa na kashe awanni da yawa a shafukan sada zumunta ko kallon fina-finai, maimakon yin ibada ko zuwa wurin wa'azi a Ramadan.

Duk da yin hakan ba za a ce ya zama laifi ba idan har mutum ya kare kansa daga ayyukan da aka haramta, amma kuskure ne duba da falala da albarkar watan.

Kara karanta wannan

Sheikh Jabir Maihula: Abubuwa 5 da ake tunanin suna karya azumi alhali ba su karyawa

Waya.
Bata lokaci a kafafen sada zumunta na hana mai azumi yin ayyukan ibada a watan azumi Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Abin da ya fi zama mai kyau shi ne mutum ya kayyade lokacin amfani da wayar hannu kuma ya fi maida hankali kan ibada, karatun Alkur’ani, da ambaton Allah.

Wata Ramadan lokaci ne da ya kamata kowane musulmi ya yi amfani da shi don gyara hali, ba don nishaɗi kawai ba.

5. Sakaci da sallar tarawihi da nafiloli

A zamanin da muke ciki, akan samu musulmi da ba sa yin sallar Tarawihi, ko dai saboda gajiya ko kuma suna tunanin ai nafila ce, ba wajibi ba ne yinta.

Tarawihi wata dama ce ta samun lada mai yawa a Ramadan. Ko da mutum ba zai iya zuwa masallaci ba, ya na da kyau ya yi nafiloli ko da kaɗan ne a gida.

Sai dai abu mafi kyau shi ne a yi sallar a bayan liman, domin manzon Allah (S.A.W) ya kwaɗaitar da yin tarawih a bayan liman har a gama.

Kara karanta wannan

Faɗa ya kaure da mutanen gari kan ruwan sha a watan azumi, an yi kisa

Sallah.
Sallar tarwaihi tana da muhimmanci da falala a addinin Musulunci Hoto: Getty
Asali: Facebook

6. Rashin haƙuri da fusata

Kamata ya yi mai azumi ya koyi haƙuri kuma ya zama mai haƙuri duba da tsadar lokaci da falalar watan a addinin Musulunci.

To sai dai ana samun masu azumi da ke da saurin fushi da faɗa, wasu kuma ba su da aiki sai gardama da yawan surutu marasa amfani a watan Ramadan.

Ku tuna cewa azumi ba kawai barin ci da sha ba ne, har da sarrafa hali. Annabi (SAW) ya ce:

"Idan ɗayanku yana azumi, kada ya yi faɗa. Idan wani ya zage shi, sai ya ce: ‘Ina azumi.’" (Sahih Bukhari).

Ana bukatar mai azumi ya kauce wa yin faɗa da gardama, ya taƙaita yawan magana matuƙar ba ambaton Allah SWT ba ne.

Abubuwa 5 da ba su karya azumi

A baya, mun kawo maku wasu abubuwa 5 da musulmai da da dama ke tunanin su na karya azumi alhali kuma ba haka ba ne.

Fitaccen malamin addinin musulmi a jihar Sakkwato, Sheikh Jabir Sani Maihula ya yi bayani kan wasu abubuwa guda 5 da ba su karya azumin Ramadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel