Yan Bindiga Sun Kutsa cikin Gida a Kano, Sun Yi Ta'asa bayan Cirewa Wani Ƴan Yatsu
- Wasu da bindiga sun kai farmaki gidan Alhaji Yusha’u Ma’aruf da ke kauyen Zakirai, karamar hukumar Gabasawa, jihar Kano da safiyar Asabar
- Maharan sun yi garkuwa da dansa Mohammed Bello Yusha’u mai shekara 20, sannan suka yanke yatsan hagu na Abubakar Yusha’u mai shekara 23
- Bayan haka, ‘yan bindigar sun kwashe wayoyi da kuma wasu kudi da ba a bayyana adadinsu ba, kafin su tsere daga wurin
- Jami’an tsaro sun fara bincike da kokarin ceto wanda aka sace tare da kama wadanda suka aikata wannan mummunan aika-aika
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.
An ce yan bindiga sun kai hari wani gida da ke kauyen Zakirai a karamar hukumar Gabasawa da ke jihar Kano.

Source: Facebook
Kano: Yadda yan sanda suka cafke yan bindiga
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da haka a shaifnsa na X inda ya ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar 9 ga watan Maris, 2025.
Hakan ya biyo bayan nasarar da yan sanda ke ci gaba da samu musamman kan masu aikata miyagun laifuffuka da kuma ƴan bindiga a jihar.
A kokarinta na dakile ayyukan ta'addanci, Rundunar ‘yan sandan a jihar Kano ta kama wasu mutum hudu da ake zargi ‘yan bindiga ne da suka fito domin siyan bindigar AK-47.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna, ne ya tabbatar da cafke su a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar 9 ga watan Maris, 2025.
A cewarsa, rundunar ta samu babban nasara wajen dakile shigowar ‘yan fashi da aikata laifuka makamanta haka a jihar.

Source: Facebook
Wasu yan bindiga sun kai hari a jihar Kano

Kara karanta wannan
Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru da misalin karfe 2:15 na dare inda maharan sun suka sace mutum guda.
Har ila yau, maharan sun yanke yatsan hagu na Abubakar Yusha’u mai shekara 23, sannan suka yi garkuwa da dan uwansa Mohammed Bello Yusha’u mai shekara 20.
‘Yan bindigar sun kuma kwashe wasu wayoyi da makudan kudi a gidan da suka kai harin kafin su tsere daga yankin.
An tabbatar da cewa jami’an tsaro sun fara farauta wadanda ake zargin domin ceton wanda aka sace saboda tabbatar da an hukunta su dai dai da laifin da suka aikata.
'Yan sanda sun cafke wasu jami'an hukumar NDLEA
A wani labarin, rundunar yan sanda a Kano ta cafke jami'an hukumar NDLEA bisa zargin harbe wata yarinya har lahira a unguwar Jaba Quarters da ke jihar.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin wanda ya kai ga rasuwar yarinyar mai shekara 19, wanda ya auku a daren ranar Laraba da ta gabata.
Kakakin hukumar NDLEA na jihar Kano, ya ce sun fara gudanar da bincike domin a iya gano haƙiƙanin abin da ya faru game da lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
