Abin Tausayi: Yaran Bello Turji Sun Sace Ɗan Isiyaka Rabiu, Matashin Ya Yi Roko a Bidiyo
- 'Yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji sun sace wani mutum da ya bayyana kansa a bidiyo a matsayin ɗan Isiyaka Rabiu, yana roƙon a biya kudin fansa
- Bidiyon da ya bayyana a kafafen sada zumunta ya nuna mutumin cikin damuwa, yana kira ga danginsa su cika sharuddan 'yan bindiga don kubutar da shi
- Rahotanni sun tabbatar cewa dan bindiga, Turji ya buya bayan farmakin sojoji, inda shi da Dan Isuhu suka tsere, ba tare da bulla a kafafen sada zumunta ba
- Sojoji sun rusa sansanonin Turji a Shinkafi, tare da cafke mayakansa da dama suka ce za su ci gaba da farmakin har sai sun kawar da 'yan ta'adda
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Wasu gungun 'yan bindiga masu biyayya ga ƙungiyar Bello Turji sun sace wani mutum da ya bayyana kansa cewa shi ɗan Isiyaka Rabiu ne.

Kara karanta wannan
Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda
A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo, matashin ya roƙi danginsa su biya kuɗin fansa don kubutar da shi ka da yan ta'addan su hallaka shi.

Source: Facebook
Matashi ya roƙi iyalan Isiyaka Rabi'u alfarma
Rahoton Zagazola Makama ya ce bidiyon da ya bayyana a kafafen sada zumunta ya nuna mutumin cikin firgici da tsoro.
A bidiyon, an gano matashin yana roƙon iyalansa su biya buƙatun waɗanda suka sace shi domin tsira da rayuwarsa.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa sacewar na da alaƙa da saura daga mabiyan Turji, waɗanda farmakin sojoji a Zamfara da makwabtanta ya raunana ƙarfinsu sosai.
A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa Bello Turji ya buya bayan da sojoji suka kai farmaki a sansanoninsa.

Source: Twitter
Yadda sojoji suka dagawa Bello Turji hankali
Masu leƙen asiri sun ce Turji da abokinsa, Dan Isuhu, sun sha da kyar a farmakin da ake kai musu wanda a yanzu yan ta'addan ke shan wuta daga rundunar sojoji.
Sabanin yadda yake alfahari a baya, Turji bai yi magana a kafafen sada zumunta ba, wanda ke nuna yadda farmakin ke masa barazana.
Jami’an tsaro sun rusa wasu sansanonin Turji a Shinkafi da wasu dazuka, tare da cafke mayaka da dama wanda ake zaton na daga cikin dalilin buyan dan ta'addan.
An ce sojoji sun sha alwashin za su ci gaba da farmakin har sai an kawar da 'yan bindiga gaba ɗaya musamman a yankin Arewacin Najeriya.
Dan bindiga, Abu Radde ya mika wuya
Kun ji cewa ana tsaka da farautar Bello Turji da kara kaimi wurin kakkabe yan ta'adda musamman a shiyyar Arewacin Najeriya, wasu rikakku sun mika wuya.
Rikakken ɗan bindiga, Abu Radde, da yaransa sun miƙa wuya ga jami’an tsaro inda suka saki mutum 10 da suka sace a yarjejeniyar zaman lafiya.
Rahotanni sun ce Abu Radde da wasu ‘yan fashi sun nemi sulhu ta hanyar lumana tare da ganawa da jami’ai a Kwari a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
