Ajali Ya Yi Kira: Hatsabibin Ɗan Bindiga, Shekau Ya Mutu yayin Arangama da Ƴan Ta'adda
- Wani daga cikin hatsabiban 'yan bindiga da yake kiran kansa da Shekau ya mutu a wajen wani kwanton-bauna
- An ce Shekau ya mutu ne yayin hari da wasu gungun 'yan bindiga na adawa suka shirya a Kachia da ke jihar Kaduna
- Majiyoyi sun ce dan bindiga, Shumo ya kai farmakin domin daukar fansa kan Shekau, wanda ya kwace makamansa
- An kashe Shekau da wasu daga cikin yaransa a kwanton-bauna da aka kai masa ranar 5 ga Maris, 2025, a kogin Narewo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Wani fitaccen dan bindiga da ake kira Shekau, saboda mugun halinsa ya mutu yayin arangama da yan bindiga.
Majiyoyi sun ce an kashe shi a kwanton-bauna da wata gungiyar ‘yan bindiga da Shumo ke jagoranta ta shirya.

Source: Original
An tsinci gawar malamin coci da aka sace
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa Shumo, wanda dan asalin Ragadada, Buruku ne a Birnin Gwari, ya kai farmakin domin ramuwar gayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan 'yan bindiga sun hallaka babban limamin cocin katolika da suka yi garkuwa da shi ranar Talata 4 ga watan Maris, 2025 a yankin Kauru a Kaduna.
Shugaban cocin a Kafanchan, Rabaran Jacob Shanet ya tabbatar da hakan ranar Laraba 5 ga watan Maris, 2025, ya roƙi matasa su kwantar da hankalinsu.
Sai dai mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kaduna, Mansir Hassan ya ce sun tura dakaru yankin domin kamo waɗanda suka yi kisan.
Yadda aka yi arangama tsakanin yan bindiga
Hakan ya biyo bayan kwace makamansa da Shekau ya yi kuma ya kashe mayakansa da dama a baya.
An tattaro cewa yayin kwanton-baunar, Shekau da wasu daga cikin mukarrabansa sun mutu a harin da aka kai ranar 5 ga Maris, 2025.

Kara karanta wannan
Ramadan: Direba ya murkushe sufetan ɗan sanda da ke bakin aiki a masallacin Abuja
An birne ‘yan bindigar da aka kashe ta hannun wasu da aka bayyana da Yellow Million da Baba Kusa.

Source: Twitter
Limami ya jagoranci sallar jana'izar 'dan bindiga
An tabbatar da cewa wani babban malamin addini ne daga kauyen Kabode a Kachia ya yi masa sallah.
Sai dai wasu yan Najeriya da dama sun kushe limamin da zai taimaka wurin birne dan ta'addan inda wasu ke zargin ko barazana aka yi masa.
Duk da haka an ce ayyukan ‘yan bindiga ya ragu a Kaduna sakamakon kokarin gwamnati da jami’an tsaro, cewar Daily Post.
An tabbatar cewa rikici tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga na karuwa tare da asarar rayuka da dama.
Sojoji sun hallaka yan bindiga a Kaduna
Mun ba ku labarin cewa dakarun sojoji sun kashe masu garkuwa da mutane biyu a Jema’a da ke jihar Kaduna, bayan sun kai dauki don ceto fasinjoji da aka sace.
An kai farmakin ne a dajin Angwan Rimi inda sojoji suka kwato bindigar AK-47, harsasai takwas, wayoyi 10 da tsabar kudi N1,136,000.
Har ila yau, an ceto mutum uku da aka sace, ciki har da Mathew Ayemowa, Tunde Salam da Mustapha Mohammed, bayan artabu da ‘yan bindiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

