Bayan Mutuwar Malamin Musulunci, Farfesa Pantami Ya Tura Sako ga Yahaya Jingir
- Farfesa Isa Ali Pantami ya shiga alhini bayan rasuwar malamin Izala, Sheikh Sa'idu Hassan Jingir, wanda aka sanar da rasuwarsa a yau Alhamis
- Pantami ya aika da ta’aziyya ga iyalan mamacin, almajiransa, ‘yan uwa da Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir tare da shugabanni baki daya a Najeriya
- Ya ce marigayin ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen addini, don haka rasuwarsa babban rashi ne ga al’umma da daukacin Musulmi
- Daga karshe, Farfesa Pantami ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya karɓi ayyukansa na alheri, ya sa ya huta a cikin Jannatul Firdaus
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya shiga alhini bayan rasuwar fitaccen malamin Izalah a yau Alhamis 6 ga watan Maris, 2025.
Pantami ya tura sakon ta'azziya ga iyalan marigayi, Sheikh Sa'idu Hassan Jingir da aka sanar ya riga mu gidan gaskiya a jihar Plateau.

Asali: Twitter
Sheikh Sa'idu Hassan Jingir ya kwanta dama
Pantami ya tura sakon ta'azziyar a yau Alhamis 6 ga watan Maris din 2025 a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar Farfesa Pantami na zuwa ne bayan sanar da rasuwar mataimakin shugaban malaman kungiyar Izala na kasa na biyu, Sheikh Sa'idu Hassan Jingir.
Sheikh Sa'idu Hassan Jingir ya shafe shekaru yana karantar da addini a jihohi da dama kafin Allah Madaukakin Sarki ya masa rasuwa a yau Alhamis 6 ga watan Maris, 2025.
Rahotanni sun ce an yi sallar jana'izarsa da misalin karfe 2:00 na rana bayan sallar Azahar a masallacin Santa, Unguwar Rimi a jihar Plateau.

Asali: Facebook
Farfesa Pantami ya kadu da rasuwar Sheikh Jingir
Farfesa Pantami ya ce tabbas an tafka babban rashi duba da gudunmawar da marigayin ya bayar.
Sheikh Pantami ya yi ta'azziya ga iyalan mamacin da almajiransa da yan uwansa da kuma Sheikh Sani Yahaya Jingir da sauran shugabanni baki daya.
Daga karshe, Pantami ya yi addu'ar Allah ya karbi ayyukansa na alheri ya kuma gafarta masa zunubansa ya sa ya huta.
Sheikh Isa Pantami a cikin sanarwar ya ce:
"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji’un!.
"Muna mika ta’aziyyarmu cikin alhini kan rasuwar daya daga cikin malamai, Shaykh Saidu Hassan Jingir, a yau.
"Muna jajantawa iyalansa, almajiransa, ‘yan uwansa da kuma Shaykh Muhammad Sani Yahya tare da sauran shugabanni baki daya.
"Allah ya karɓi ayyukansa na alheri, ya gafarta masa, ya sa ya huta a Jannatul Firdaus tare da iyaye, malamai da ‘yan uwa."
Atiku ya jajanta bayan mutuwar Malamin Musulunci
Kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi jimamin mutuwar babban malamin Musulunci a jihar Adamawa.
Atiku ya yi ta'aziyyar bayan mutuwar Sheikh Ibrahim Abubakar Daware wanda a cewarsa ya ba da gudunmawa sosai wurin koyarwar Musulunci.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce marigayin ya taba shugabantar Firyanul Islam Adamawa kuma fitaccen malami ne da ya san fikihu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng