Gwamna Ya Jawo Mawakan Kannywood, Sun Yi Watsi da Barau Sun Koma Kwankwasiyya

Gwamna Ya Jawo Mawakan Kannywood, Sun Yi Watsi da Barau Sun Koma Kwankwasiyya

  • Wasu fitattun mawakan Kannywood da suka bar tafiyar Kwankwasiyya sun gana da Mai girma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
  • Mawakan da suka hada da Nazifi Asnanic, Ali Jita, da wasu ‘yan wasan kwaikwayo sun samu jagorancin Abba Al Mustapha
  • A karin hasken da ya yi, Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Kano ya ce mawakan sun sauya shawara ne bisa wasu dalilai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoWasu daga cikin mawakan Kannywood da masu wasan barkwanci da suka sauya sheka zuwa APC ta hannun Sanata Barau Jibrin sun canja shawara.

A yammacin Talata ne aka hango mawakan da sauran ‘yan Kannywood a gidan gwamnatin Kano, bisa jagorancin shugaban hukumar tace fina-finai da dab’i, Abba Al Mustapha.

Kara karanta wannan

Faransa ta fara zartar da yarjeniyar da ta yi da Tinubu a Najeriya

Kwankwasiyya
Mawakan Kannywood sun koma Kwankwasiyya Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook

A bidiyon da aka wallafa a shafin Facebook na Kwankwasiyya Reporters, Abba Al Mustapha ya bayyana cewa ‘yan Kannywood din sun dawo gida ne saboda kishin al’umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan Kannywood sun koma Kwankwasiyya

‘Yan Kannywood da suka hada da Ali Jita, Habu Tabule, Sarkin Waka, Nazifi Asnanic, da Abale sun gana da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf bisa jagorancin Abba Al Mustapha.

A karin bayanin da ya yi bayan komawar abokansa zuwa Kwankwasiyya, shugaban hukumar tace fina-finai, ya bayyana cewa mawakan da sauran ‘yan fim sun gana da gwamna.

Ya ce:

"Mun hadu, an yi hira, an ci abinci, an sha ruwa, an dauki hotuna da mai girma gwamna, Injiniya Abba Kabir Yusuf. Kuma za a ji mamakin cewa kamar wadannan mutanen sun dan yi bankwana da siyasar gidan Kwankwasiyya.
Gwamna ya zauna tare da mu, ana ta annashuwa, aka fahimci juna, ya ba mu shawarwari.”

Kara karanta wannan

Rigimar ciyamomi ta hana gwamnan PDP sukuni, ya je neman mafita wajen jigon APC

Dalilin ‘Yan Kannywood na komawa Kwankwasiyya

Abba Al Mustapha ya bayyana cewa siyasa mai kyau ta ginu ne a kan gina rayuwar jama’a da taimakon al’umma, ba daidaikun mutane ba.

Kwankwasiyya
Za a ci gaba da kokarin dawo da 'yan Kannywood cikin Kwankwasiyya Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook

Ya ce ‘yan Kannywood da suka koma gidan Barau a APC a baya sun yi wa kansu fada, domin akidar da suka tarar a can ba ta kai tsarin da Kwankwasiyya ke tafiya a kai ba.

Abba Al Mustapha ya ce:

"Duk wanda suka fita daga cikin tsarinmu, In Sha Allahu za mu bi su, mu zauna mu tattauna. Duk rigima ko duk wani abu da aka yi, za mu iya gyara shi a kan tebur.”

Ya nanata cewa duk dan Kwankwasiyya yana da kishin al’umma, wanda ya sa wadanda suka fice suka sauya shawara domin dawowa tafiyar gwamnatin Abba Kabir Yusuf, wacce za ta ciyar da al’umma gaba.

Fitattun 'yan Kannywood sun koma APC

A baya, kun samu labarin cewa shahararren mawaki Nura M. Inuwa ya sauya sheka daga NNPP Kwankwasiyya zuwa jam’iyyar APC karkashin jagorancin Sanata Barau Jibrin.

Kara karanta wannan

'An yi zalunci': Shekarau ya fadi alakarsa da Kwankwaso bayan tono abin da ya faru tsakaninsu

Sanata Barau, wanda shi ne Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya karbi mawakin ne da Fati Muhammad da wasu fitattun ‘yan wasan kwaikwayo a ziyarar da suka kai masa Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng