Ramadan: Babban Limami Ya Soki Gwamnonin Arewa kan Rufe Makarantu, Ya Fadi Kuskurensu
- Babban limamin Edo, Abdulfattah Enabulele ya taɓo batun rufe makarantu da wasu gwamnonin jihohin Arewa suka yi
- Malamin addinin musuluncin ya soki matakin rufe makarantun inda ya bayyana cewa ko kaɗan hakan bai dace ba
- Ya bayyana rufe makarantun ba koyarwar addinin Musulunci ba ne, domin ana son Musulmi ya nemi ilmi a kowane hali
- Sheikh Abdulfattah ya nuna cewa rufe makarantun da gwamnonin suka yi, zai hana ɗalibai samun ilmin da ya kamata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Babban limamin Benin, Sheikh Abdulfattah Enabulele, ya yi magana kan kulle makarantu da wasu gwamnonin jihohin Arewa suka yi saboda azumin Ramadan.
Malamin addinin Musuluncin ya nuna rashin amincewarsa ga matakin rufe makarantu na tsawon makonni biyar da gwamnonin suka ɗauka.

Source: Facebook
Sheikh Abdulfattah Enabulele ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a birnin Benin, babban birnin jihar Edo a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a manta ba dai gwamnonin jihohin Bauchi, Katsina, Kano, da Kebbi sun bada umarnin rufe makarantu don bayar da damar yin azumin Ramadan.
Malamin addini ya soki rufe makarantu
Sheikh Abdulfattah Enabulele ya bayyana cewa rufe makarantu don Ramadan ba koyarwar addinin Musulunci ba ne.
A cewarsa, Musulunci yana ƙarfafa neman ilmi a kowanne hali, saboda haka bai kamata a rufe makarantu gaba ɗaya ba.
Ya ce abin da ya dace shi ne a rufe makarantun da ƙarfe 12:00 na rana, amma ba a rufe su gaba ɗaya ba.
"Wannan ba koyarwar addinin Musulunci ba ne. Babu wata aya a cikin Al-Qur’ani ko hadisin Annabi Muhammad (SAW) da ke goyon bayan wannan ɗabi’a. Ya kamata mu zama masu hangen nesa, mu girmama kanmu."
"Musulmi su fahimta cewa azumi ba yana nufin mutum ya zauna ya kwanta ya yi ta barci ba, dole ne ka fita ka nemi abin dogaro da rayuwa."
"Don haka, kar a rufe makarantu saboda ana azumi. Idan ana son taimakawa ɗalibai, a bar su su je makaranta su taso da ƙarfe 12:00 na rana."
"Dole ne mu ci gaba da neman ilmi, kuma muna ganin malamai suna zuwa talabijin da rediyo suna karantar da Al-Qur’ani, wannan ma ilmi ne."
- Sheikh Abdulfattah Enabulele
Sheikh Enabulele Ya faɗi illar rufe makarantun
Ya jaddada cewa rufe makarantun zai hana ɗalibai damar samun ilmi.
"Me suke zuwa yi a makaranta? Ba neman ilmi ba ne? Rufe makarantun bai da ma’ana, domin Musulunci yana koyar da cewa a lokacin azumi ma ana ci gaba da neman ilmi."
"Ilmi wata hanya ce ta ƙarfafa mutum, don haka ya kamata mu ƙarfafa wa ƴaƴanmu gwiwa su nemi ilimi. Ni ba na goyon bayan rufe makarantu a lokacin Ramadan, kuma Musulunci ma bai goyi bayan hakan ba."
- Sheikh Abdulfattah Enabulele
Gwamnoni sun yi wa CAN martani
A wanu labarin kuma, kun ji cewa gwamnatocin jihohin Arewa sun yi martani mai zafi ga ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) kan batun rufe makarantu a watan azumin Ramadan.

Kara karanta wannan
'Gwamnonin Arewa wawaye ne': Sowore ya yi kakkausar suka kan rufe makarantu a Ramadan
Gwamnatocin sun bayyana cewa babu gudu babu ja da baya kan batun rufe makarantun a lokacin azumin watan Ramadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

