Gwamna Ya Fadi Sharadin Karban Tuban 'Yan Ta'adda irinsu Bello Turji

Gwamna Ya Fadi Sharadin Karban Tuban 'Yan Ta'adda irinsu Bello Turji

  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta nemi ‘yan ta’adda a daji domin yin sulhu ba
  • Dikko Radda ya bayyana haka ne yayin wani shirin tallafawa al’umma da aka gudanar a karamar hukumar Jibiya
  • Haka zalika, an kaddamar da shirin tallafin Naira miliyan 50 ga matasa, mata tsofaffi, da mabukata a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta nemi ‘yan ta’adda a daji domin sulhu ba sai dai idan sun mika wuya da kansu.

Ya bayyana haka ne yayin taron tallafawa al’umma da aka gudanar a karamar hukumar Jibiya, inda ya kaddamar da shirin bada tallafin Naira miliyan 50.

Kara karanta wannan

Neman lalata: Majalisa ta yi watsi da bukatar Natasha kan zargin Akpabio

Radda
Gwamna Radda ya ki yarda da maganar sulhu da 'yan bindiga. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya wallafa a Facebook ta nuna cewa tallafin an shirya shi ne domin rage radadi ga jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ba maganar sulhu da 'yan ta'adda' - Gwamna Radda

Gwamna Dikko Radda ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta nemi ‘yan ta’adda a daji domin yin sulhu da su ba.

Sai dai ya bayyana cewa, idan sun tuba da gaske kuma sun yanke shawarar daina ta’addanci, gwamnati za ta rungume su a matsayin ‘yan kasa na gari.

“Idan ‘yan ta’adda sun ajiye makamansu kuma sun shirya su zama masu bin doka, muna da shirin sake shigar da su cikin al’umma,”

- Dikko Radda

Ya kuma yaba wa kokarin jami’an tsaro da shugabannin yankin Jibiya wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Hakan na nuni da cewa idan 'yan bindiga kamar su Bello Turji da sauransu suka ajiye makamai suka mika wuya za a iya karbar tubansu.

Kara karanta wannan

Yadda Biden da Amurka su ka matsawa Najeriya lamba, aka saki jami'in Binance

An raba tallafi ga matanen Jibiya

A yayin taron, an kaddamar da shirin bada tallafin Naira miliyan 50 domin rage wahalhalun da mata, matasa da mabukata ke fuskanta a lokacin azumin Ramadan.

Tallafi da dan majalisar jiha mai wakiltar Jibiya Hon. Mustapha Yusuf ya shirya, ya samu goyon bayan jagororin jam’iyyar APC a yankin.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri ya yi daidai da tsarin jin kai na gwamnatinsa, musamman shirin ciyar da mutane 72,000 a kullum a watan Ramadan.

Radda
Gwamnan Katsina yayin bude Rumbun Sauki a jihar. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Dikko Radda ya ce an shirya ciyar da kimanin mutum miliyan 2.2 kafin karshen Ramadan, domin rage radadin da jama’a ke fuskanta.

Bukatar hadin kai domin inganta tsaro

Gwamna Radda ya jaddada cewa shugabanci yana bukatar hadin gwiwa domin magance matsalolin al’umma.

Ya bukaci hadin kai tsakanin shugabanni da al’umma wajen shawo kan matsalolin tsaro da talauci.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Nasir Yahaya Daura, ya yaba wa Hon. Yusuf bisa wannan tallafi da ya bayar ga mabukata.

Taron ya samu halartar manyan kusoshin gwamnati, ‘yan majalisa da shugabannin jam’iyyar APC a yankin.

An rusa gidan 'yan bindiga a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Edo ta dauki matakin rusa gidajen masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun nuna cewa an kama mutane biyu cikin masu garkuwa da mutanen kuma sun bayyana yadda suke sace al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel