Borno: Boko Haram Sun Yi Watsi Da Fansar $50,000, Sun Cigaba da Tsare Iyalan Alkali
- ‘Yan ta'addan Boko Haram da suka sace alkalin babbar kotun jihar Borno, Mai Shari'a Haruna Mshelia, da iyalansa sun gindaya kudin fansa
- An saki alkalin ne bayan an biya tarin kudin fansa, amma ‘yan ta'addan sun ci gaba da riƙe matarsa, Binta Othman, wacce ita ma alkaliya ce
- Haka kuma, Boko Haram har yanzu tana riƙe da mai gadin alkalin da direbansa, waɗanda aka sace tare tun watan Yuni, shekarar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - 'Yan ta'addan Boko Haram sun bukaci kudin fansa na $500,000 domin sakin matar Mai Shari'a Haruna Mshelia da dan sandan da ke gadin sa, da kuma direbansa.
Wata majiya daga cikin iyalan ta ce, 'yan ta'addan sun ki amincewa da tayin farko na $50,000 da aka yi masu, sun nace cewa dole ne a biya $500,000 kafin sakin wadanda ke hannunsu.

Kara karanta wannan
Sojoji da ‘yan ta’adda sun gwabza bayan harin ofishin ‘yan sanda, an samu asarar rayuka

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa, an sace Mai Shari'a Mshelia a ranar 24 ga watan Yuni, 2024, tare da matarsa, Binta Othman, wacce ita ma alkaliya ce a kotun Wulari da ke Maiduguri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Boko Haram sun saki alkali Mshelia
‘Yan ta’addan sun saki Mai Shari'a Mshelia a ranar 8 ga Satumba bayan an biya kudin fansa mai yawa, amma sun gindaya sharadin cewa dole ne a basu karin $500,000 domin a saki iyalinsa.
Wata majiya daga iyalin ta ce:
“Muna da labarin cewa iyalin sun iya hada kusan $50,000, amma ‘yan ta’addan sun yi watsi da tayin, suna nacewa a biya $500,000 da suka bukata.”
Boko Haram: ‘Yan sanda sun yi magana kan kudin fansa
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta Borno, ASP Nahum Daso, domin jin karin bayani kan halin da ake ciki game da ‘yan sandan da aka sace, ya ce yana bukatar lokaci kafin ya yi bayani.

Asali: UGC
An kuma yi kokarin jin ta bakin Justice Haruna Mshelia, alkalin babbar kotun Borno da 'yan bindiga su ka saki, amma ba a samu damar jin karin bayani daga gare shi ba.
Boko Haram na cigaba da tsare Farfesan NAUB
A daya bangaren, har yanzu ‘yan Boko Haram suna tsare da Farfesa Abubakar Eljuma, Shugaban Sashen Kimiyya da Fasaha a Jami’ar Soja ta Najeriya da ke Biu (NAUB).
Majiyoyi daga jami’ar sun ce har yanzu wadanda suka sace shi ba su tuntubi jami’ar ko iyalinsa ba dangane da halin da yake ciki ko neman kudin fansa.
Dakaru sun hallaka kwamandojin Boko Haram
A wani labarin, kun ji cewa Sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a yaki da ta’addanci bayan sun hallaka akalla ‘yan Boko Haram guda tara a wani samame da suka kai a jihar Borno.
Daga cikin wadanda aka kashe har da Amirul Bumma, wanda ake zargin shi ne babban mai haɗa bama-baman da ƙungiyar Boko Haram ke amfani da su wajen hallaka bayin Allah.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng