Sadu da Shugaban MTN, Mutum na 1 da Ya Fi Kwasar Albashi a Najeriya, An Gano Kuɗin da Yake Samu
Lagos - Shugaban MTN Nigeria, kamfanin sadarwa mafi girma a Najeriya, Karl Toriola yana cikin fitattun shugabanni a ɓangaren kasuwanci a ƙasar nan.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Mista Toriola shi ne mutum na farko a jerin shugabannin kamfanoni masu zaman kansu da suka fi ɗibar albashi a wata a Najeriya.

Source: Twitter
A wata kididdiga da Jobs Region ta wallafa a shafin X, shugaban MTN na Najeriya shi ne na ɗaya a jerin shugabannin kamfanonin da suka fi dibar albashi, ana biyansa Naira miliyan 850 duk wata.
Haka nan a rahoton Naira Metrics, yana cikin jerin shugabannin kamfanoni mafi samun albashi a Najeriya, tare da sunaye irin su Ebenezer Onyeagwu da Seun Agbaje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin karatun Karl Toriola
An haifi Karl Olutokun Toriola a ranar 16 ga Maris, 1972, a garin Ife, da ke jihar Osun a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Ya girma a garin Modakeke kuma a nan ya samu ya kammala karatun firamare da sakandare.
Bayan haka, ya shiga Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife, ya kammala digirinsa na farko a fannin injiniya watau Electrical Engineering a 1994.
Daga nan, ya zarce zuwa Jami’ar Wales da ke birnin Swansea a Birtaniya, kuma a nan ya samu digiri na biyu a fannin tsare-tsaren sadarwa (Communication Systems) a 1996.
Bayan haka, Toriola ya ci gaba da zurfafa iliminsa a harkokin da suka shafi shugabanci da kasuwanci ta hanyar halartar manyan makarantu kamar:
- Harvard Business School (2005–2008)
- Institute of Management Development (IMD), Switzerland (2006)
- London Business School (2009)
- Wharton Business School (2011)
- INSEAD, Singapore (2013)
Matakan da Karl Toriola ya taka a fannin sadarwa
Toriola ya fara aiki a bangaren sadarwa a 1995 a kamfanin Ericsson Switzerland, ya kwashe shekaru biyar a nan kafin ya koma kamfanin Ericsson Nigeria a 2000 a matsayin Manajan sashin GSM.
A wancan lokaci, an fara bunkasa harkar sadarwa a Najeriya, kuma ƙwarewarsa ta taka rawa sosai.

Source: UGC
A 2004, ya koma Vmobile Nigeria (Airtel Nigeria a yanzu) a matsayin shugaban sashen ayyuka, ya taimaka wajen bunkasa tsarin fasahar kamfanin. A 2006, ya bar Vmobile.
A wanna shekara 2006, Toriola ya koma kamfanin MTN Irancell a Tehran, Iran, a matsayin mai bada shawara kan ayyukan sadarwa, ya kawo masu ci gaba a hanyoyin sadarwa.
Daga baya, aka dawo da shi MTN Nigeria a matsayin babban jami’in fasaha (CTO) a Oktoba 2006. A karkashinsa, MTN ya samu lambar yabo ta Best CTO da Best Network a 2009.
Daga nan, ya zama shugaban MTN na Kamaru a 2011, a lokacin ya ƙara yawan abokan hulɗar kamfanin daga 51% zuwa 62%, ya tabbatar da lasisin 3G da 4G, kuma ya taimaki gwamnatin kamaru ta mallaki wani kaso na WACS.
A 2015, Karl Toriola ya samu ƙaɗin girma zuwa shugaban gudanarwa na rukunin kamfanonin MTN Group mai kula da ayyukan kamfanin a ƙasashe 12.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya ware sama da Naira biliyan 700 a watan azumi, za a yi muhimman ayyuka
Bayan shekara guda, ya zama mataimakin shugaba na Yammacin da Tsakiyar Afirka.
A watan Oktoba 2020, aka naɗa shi a matsayin shugaban MTN Nigeira, ya gaji Ferdinand Moolman, ya fara aiki a matsayin CEO a ranar 1 ga Maris, 2021.
Muƙamai da kwamitocin da yake ciki
Baya ga mukaminsa na shugabancin MTN Nigeria, Toriola yana da mukamai a wasu hukumomi da kwamitoci, ciki har da:
- Shugaban MTN/Areeba Guinea
- Darakta a kamfanin Jumia Africa
- Darakta a American Towers Uganda
- Darakta a wasu rassan MTN a kasashen Faransanci na Afirka.
Shugaban MTN ya zama na 1 a ɗibar albashi
Karl Toriola ya nuna kyakkyawan tsari na kwarewa, kirkire-kirkire, da juriya, wanda ya sanya shi cikin jerin shugabannin kamfanoni mafi samun albashi a Najeriya.
Ƙwarewarsa wajen inganta ci gaba, kulla yarjejeniya, da daidaita ayyukan kamfanoni ya kara tabbatar da shi a matsayin jigo a bangaren sadarwa da kasuwanci a Najeriya.
NCC ta amince da ƙarin kudin kira
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sahalewa kamfanonin sadarwa su ƙara kaso 50% na kuɗin kira. data da tura saƙo.
Wasu ‘yan Najeriya sun koka a kan yadda ake fama da matsalar sabis din waya, sannan kuma aka samar da sabon karin farashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


