Gwamnatoci Sun Yi Zazzafan Martani ga Kiristoci kan Rufe Makarantu a Azumi

Gwamnatoci Sun Yi Zazzafan Martani ga Kiristoci kan Rufe Makarantu a Azumi

  • Gwamnatocin jihohin Kebbi, Bauchi da Kano sun bayyana cewa ba za su sauya matsayar rufe makarantu a watan Ramadan ba
  • Gwamnatin Kebbi ta ce an yanke hukuncin ne bayan tuntubar shugabannin addinai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki
  • Bauchi da Kano sun jaddada cewa hutun Ramadan na cikin tsarin shekarar karatu, kuma ba zai kawo cikas ga dalibai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Gwamnatocin jihohin Kebbi, Bauchi da Kano sun tabbatar da cewa hutun Ramadan da aka bai wa makarantun firamare da sakandare zai ci gaba da kasancewa kamar yadda aka tsara.

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta nuna damuwa kan rufe makarantun a lokacin azumi.

Kara karanta wannan

Ana ciyar da mabukata a Kano, mutane 91,000 za su samu buda-bakin Ramadan

Jihohi
Gwamnatocin Arewa sun yi martani ga CAN a kan rufe makarantu a Ramadan. Hoto: Lawal Muazu Bauchi| Abba Kabir Yusuf|Nasir Idris
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa gwamnatin Kebbi ta ce an cimma matsayar ne bayan tattaunawa da dukkan bangarorin da abin ya shafa, ciki har da shugabannin addinai da iyaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kebbi ta ce ba za ta sauya matsayar hutu ba

Mai magana da yawun gwamnan Kebbi, Ahmed Idris, ya bayyana cewa an yanke hukuncin ne bayan shawarwari da shugabannin addinai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewar hadimin gwamnan:

"Akwai taruka da aka gudanar da shugabannin addinai da iyaye kafin a cimma matsaya. Saboda haka, ba za mu sauya wannan hukunci ba,"

Ya kara da cewa hutun Ramadan ba zai shafi fiye da makonni biyu na jadawalin karatun dalibai ba, don haka ba zai haifar da tangarda ga tsarin karatu ba.

Martanin jihar Kano ga kungiyar CAN

A jihar Kano, Daraktan Fadakarwa na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Kiru, ya ce babu dalilin sauya wannan hukunci saboda an dauki matakin ne tare da amincewar duk masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Dalibai sun fusata kan rufe makarantu a Arewa, NANS ta shirya zanga-zanga

"An yi taron masu ruwa da tsaki a matakin tarayya wanda kungiyar CAN da sauran kungiyoyi suka halarta,"

- Balarabe Kiru

Ya kara da cewa majalisar zartarwar jihar ta Kano ta amince da wannan hutun tun a farko, don haka ba za a canza matsayar ba.

"Hutun na cikin tsarin karatu" - Bauchi

Kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi, Lawal Zayam, ya bayyana cewa hutun Ramadan yana cikin tsarin shekarar karatu tun farkon zangon 2024/2025.

"Ba mu dauki matakin da bai bisa tsari ba.
"Kafin a tsara kalandar shekarar karatu, an yi shawarwari da masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin makarantun masu zaman kansu,"

- Lawal Zayam

Ya kara da cewa an yi hadin gwiwa da wasu jihohi domin tabbatar da daidaito kafin a amince da wannan hutun.

Shugaban CAN
Shugaban CAN a Najeriya. Hoto: @presidentofCAN.
Asali: Twitter

Gwamnatocin jihohin sun yi martanin ne bayan kungiyar Kiristoci ta bukaci a janye hutun azumi da aka bayar a jihohin.

Kara karanta wannan

Ramadan: CAN za ta yi shari'a da jihohin da suka rufe makarantu, ta kafa sharuda

Tasirin hutun Ramadan ga dalibai da tsarin karatu

Hutun Ramadan da gwamnatocin jihohin Kebbi, Bauchi da Kano suka amince da shi yana da tasiri mai yawa ga dalibai da tsarin karatu.

A cewar hukumomi, hutun ba zai haifar da cikas ga jadawalin karatu ba, domin yana daga cikin tsarin shekarar karatu tun farko.

Sai dai, wasu masu sharhi sun bayyana damuwarsu kan yadda hutun ka iya rage lokacin koyarwa, musamman ga dalibai masu shirin rubuta jarrabawar karshe.

A wasu bangarori kuma, iyaye da malamai sun nuna goyon baya, suna masu cewa hutun zai bai wa yara damar gudanar da ibada cikin nutsuwa.

Duk da ce-ce-ku-cen da ake yi, gwamnatin jihohin sun jaddada cewa matakin ya samo asali ne daga shawarwari da bangarori daban-daban, ciki har da shugabannin addinai da iyaye.

Wannan na nuna cewa ana kokarin daidaita bukatun karatu da na addini domin samar da ingantaccen yanayi ga kowa.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna ya rufe dukkanin makarantun jiharsa na tsawon mako 5

An raba tallafin Ramadan a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar dokokin jihar Kano, Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa ya raba tallafin azumin watan Ramadan a mazabarsa.

Kofa ya raba tallafin kudi da kayan koyon sana'a ga matasa maza da mata domin samun abin dogaro da kai da rage zaman kashe wando a mazabarsa.

'Yan siyasa da masu hannu da shuni kan dauki nauyin ciyarwa da tallafawa masu karamin karfi a cikin watan Ramadan, wanda ke kara masu kusanci da talakawan da ke kusa da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng