Ana Ciyar da Mabukata a Kano, Mutane 91,000 za Su Samu Buda Bakin Ramadan

Ana Ciyar da Mabukata a Kano, Mutane 91,000 za Su Samu Buda Bakin Ramadan

  • Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyar da masu karamin karfi kullum yayin da aka fara azumin watan Ramadan
  • Mataimakin gwamna, Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya kaddamar da ciyarwar a ranar Litinin, ya ce mutum 91,000 za su amfana
  • Kwamred ya bayyana cewa an dauki matakan da za su tabbatar da cewa an samar da abinci mai inganci na tsawon kwanaki 27

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya kaddamar da shirin ciyar wa da azumi na shekarar 2025 a jihar a ranar Litinin.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bullo da shirin ciyar da azumi domin tallafa wa mabukata ta hanyar samar da abinci na buda-baki a duk tsawon watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya yi gargadi kan siyasantar da tsaro bayan kalaman El-Rufa'i

Gwamna
An kaddamar da ciyarwar azumi a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf/Ibrahim Adam
Asali: Facebook

Jaridar Leadership News ta ruwaito cewa a bana, shirin zai amfanar da mutane 91,000 da ke cikin mawuyacin hali a fadin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gwamnatin Kano na ciyarwar azumi

The Guardian ta wallafa cewa gwamnatin Kano ta bayyana cewa shirin ciyarwar azumi na bana wani bangare ne na kokarinta na rage wahalhalun da al’ummar dake azumi ke fuskanta.

Yayin kaddamar da shirin, Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya bayyana cewa:

“Wannan shiri na shekara-shekara na daga cikin shirye-shiryen jin kai da gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin rage wahalhalun da masu azumi ke fuskanta.”
Ibrahim
Mutum 91,000 ne za su samu buda baki a Kano Hoto: Ibrahim Adam
Asali: Facebook

Ya ci gaba da cewa:

“Sanin irin bukatun da al’ummar jihar ke da su a lokacin Ramadan, shi ya sa gwamnatin Kano ta kuduri aniyar ganin an tallafa wa mabukata ta hanyar ciyar da su.”
“Saboda haka, gwamnati ta amince da shirin ciyar da azumi na 2025, tare da kebe cibiyoyi 91 da za a raba abinci a fadin jihar."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kudin ciyarwa a Ramadan, ta fadi abin da za ta kashe

Kano: Za a ciyar da mutane 91,000

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa shirin ciyar da azumi na bana zai raba abinci ga mutane 91,000 a kullum, tsawon kwanaki 27 a cibiyoyi 91 da aka tanada a fadin jihar.

Domin tabbatar da ingantaccen aiwatar da shirin, gwamnati ta ce an dauki kamfanonin dafa abinci don samar da kwanon abinci 91,000 domin kai wa cibiyoyin da aka tanada.

Mataimakin Gwamnan Kano, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin ciyarwar azumi na shekarar, ya bayyana gamsuwa da yadda aka fara aiwatar da shirin cikin nasara.

Ya kuma bukaci kamfanonin da ke da alhakin samar da abinci da su tabbatar da kai abinci a kan lokaci da kuma a ingantacciyar hanya domin cimma manufar shirin.

Miji ya kashe matarsa saboda abincin azumi

A baya, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kama wani magidanci, Alhaji Nuru Isa bisa zargin hallaka matarsa, Wasila Abdullahi saboda abincin azumi.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna ya rufe dukkanin makarantun jiharsa na tsawon mako 5

Ana zargin magidancin mai shekaru 50 da yi wa matarsa mai shekaru 25 dukan kawo wuka, bayan an samu takaddama a kan yadda za a raba kayan marmarin da za a sha da bude baki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel